Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 15:36:41    
Bayani kan Malam Lu Bolun, babban manajan hotel din Hilton na birnin Hefei na kasar Sin

cri

Malam Lu Bolun ya kara da cewa, a unguwoyin birnin Hefei, ya kasance tafkoki da duwatsu da dakunan Ibada da sauran tsofaffin kayayyakin al'adu masu daraja kwarai. A ganinsa, tarihin wata kasa da al'adunta tushe ne ga raya ta. Yayin da ake bunkasa tattalin arziki cikin sauri, wajibi ne, a dora muhimmanci sosai ga al'adun gargajiya. Ya ci gaba da cewa, "ina sha'awar al'adun gargajiyar kasar Sin kwarai. Idan babu kyawawan al'adu, to, ko ta yaya ba za a bunkasa wata kasa ba. Haka kuma idan an soke irin wannan darajar al'adun gargajiya, to, za a soke tarihi ke nan, wannan abu ne mai nadama kwarai."

Malam Lu Bolun yana sha'awar yin hira da yawon shakatawa tare da abokansa Sinawa don more idanu da kyawawan wurare na kasar Sin, da dadana abinci mai dadin ainun.

Yanzu Malam Lu Bolun yana kaunar zamansa a birnin Hefei. Ya ce, birnin Hefei birni ne na zamani wanda ke kiyaye al'adun gargajiya sosai. Ya hakake cewa, birnin yana da kyakkyawar makomarta wajen samun bunkasuwa a nan gaba. (Halilu)


1 2