Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-07 15:36:41    
Bayani kan Malam Lu Bolun, babban manajan hotel din Hilton na birnin Hefei na kasar Sin

cri

Malam Lu Bolun ya zo kasar Sin ne daga kasar Belgium, yanzu shi ne babban manajan Hotel din Hilton a birnin Hefei, fadar gwamnatin lardin Anhui na kasar Sin. Ya kware sosai wajen kula da kyakkyawar hotel mai taurari biyar, kuma yana sha'awar al'adun kasar Sin ainun.

Malam Lu Bolun ya shafe shekaru 15 yana aiki domin kamfanin Hilton. Bayan da kamfaninsa ya nada shi don ya zama babban manajan Hotel din Hilton a birnin Hefei, sai ya zo birnin a watan Agusta na shekarar bara, ya fara gudanar da harkokin wannan sabuwar hotel.

Da Malam Lu Bolun ya tabo magana a kan dalilin gina hotel dinsa a birnin Hefei, sai ya bayyana cewa, "yanzu ana bunkasa tattalin arzikin kasar Sin cikin sauri sosai, mun ganam ma idanunmu irin babban ci gaban da ake samu a birnin Hefei da sauran birane daban daban na kasar. Yayin da na sauka birnin Hefei, na zauna a kan hawa ta 24 ta hotel, na ga sabbin manyan gine-gine da yawa da aka gina a birnin ba da dadewa ba. Sabbin kamfanonin da ke zuba jari a birnin suna da yawa. Yau sama da rabin shekarar da aka fara aiki da hotel dinmu, an riga an shirya manyan tarurrukan tattaunawa kan ayyukan zuba jari har sau biyu a birnin. Kyakkyawan yanayin zuba jari ya jawo hankulan 'yan kasuwa da yawa da su zuba jari a birnin, lale, wannan ma kyakkyawar dama ce ga Hotel din Hilton mai bauta wa 'yan kasuwa. "

Bisa matsayinsa na babban manajan hotel, Malam Lu Bolun ya kan yi aiki mai yawa a ko wace rana, ya yi rangadin aiki a hotel da safe, ya sadu da baki, ya fahimci abubuwan da baki ke bukata. Bayan haka bi da bi ya kan gana da manajojin sassa daban daban a ko wace rana, ya san matsalolinsu, ya kuma tattauna tare da su a kan hanyar da za a bi wajen daidaita matsalolin da tsara shirin bunkasuwa.

Bayan lokacin aikinsa, Malam Lu Bolun ya kan yi kokari sosai wajen fahimtar kasar Sin. Ya ce, kafin zuwansa a kasar Sin, a ganinsa kasar Sin kasa ce ta gargajiya sosai. Ya gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa, "kafin na zo kasar Sin, na fahimci wasu abubuwan kasar Sin ne ta telebijin da littattafai, kuma na taba ganin wasu tsofaffin hotunan kasar Sin. Wadannan tsofaffin hotunan sun nuna yadda Sinawa ke kan kekunan hawa."


1 2