Abin da ya cancanci a lura da shi shi ne, kashegari da aka kashe wannan jami'in kasar Amurka a kasar Sudan, Bush ya sake sa hannu a kan umurni don amincewa da hukumomin jihohi daban daban na Amurka da kananan hukumominta su daina zuba jari ga kamfanoni wadanda ke da alaka da harkokin da ake yi a fannonin man fetur da makamashi na kasar Sudan, sa'an nan wasu kamfanonin zuba jari na kasar Amurka su ma za su daina aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci a tsakaninsu da kamfanoni da ke da alaka da manyan harkokin tsimi na kasar Sudan kafin lokacin ya cika, kuma ba za a yanke musu hukunci ba.
Bayan aukuwar al'amarin kisan gillar, wasu kafofin watsa labaru na kasar Sudan sun yi tsammani cewa, mai yiwuwa ne al'amarin na da alaka da kungiyar Al-Qaida. Sun nuna cewa, Osama Bin Laden, madugun kungiyar Al-Qaida da mtaimakinsa Ayman Al-Zawahri sun taba yin kira ga kasar Sudan da ta yi yakin jihadi a kan kasashen yammaci.
Amma ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sudan ta bayar da sanarwa cewa, wannan harbi da aka yi ba harin ta'addanci ba ne, kuma wannan wani al'amari ne da bai danganci harkokin siyasa ba. Sanarwar ta jaddada cewa, kullum gwamnatin kasar Sudan tana yin kokari sosai wajen kiyaye zaman lafiyar 'yan kasashen waje musamman 'yan diplomasiya da ke zama a kasar Sudan. Hukumomin kasar Sudan sun riga sun fara yin bincike a kan al'amarin nan, kuma ko ba dade ko ba jima za a yanke wa masu laifin hukunci yadda ya kamata. (Halilu) 1 2
|