Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-02 16:04:07    
An yi wa wani jami'in diplomasiya na kasar Amurka kisan gilla a kasar Sudan

cri

Ran 1 ga wata, a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, an yi bata kashi kan wani jami'in diplomasiya na kasar Amurka da ke a kasar Sudan. Wannan ne karo na farko da aka yi wa 'yan diplomasiya na kasashen waje a kasar Sudan kisan gilla a cikin shekarun nan da suka gabata.

Wannan al'amarin kisan gilla ya auku ne da karfe 4 na safiyar ran nan. A lokacin, wasu dakaru wadanda ba a san su wane ne ba suka kai hari a kan wata motar ofishin jakada na kasar Amurka a kan wata babbar hanyar birnin Khartoum, nan take direban motar dan kasar Sudan ya mutu, haka kuma wani jami'in hukumar raya kasa da kasa ta Amurka wanda aka harbe shi sau da dama shi ma ya mutu, bayan da aka kwantar da shi a asibiti. Ya zuwa yanzu, babu wata kungiya ko wani mutum da ta amince da daukar alhakin kai wannan hari.

Kafofin watsa labaru suna ganin cewa, ko shakka babu, wannan al'amari zai kara tsananta hulda mai zafi da ke tsakanin kasashen Amurka da Sudan. Tun bayan shekarar 1990, huldar da ke tsakanin kasashen biyu ta yi ta tsami sosai. Kasar Amurka ta zargi gwamnatin kasar Sudan da nuna goyon baya ga ta'addancin duniya da yi wa kabila kisan kiyashi a yankin Darfur. Amma gwamnatin kasar Sudan ta tsaya tsayin daka wajen musanta zargin da Amurka ta yi mata. A shekarar 1998, kasar Amurka ta yi sanadiyyar surutun baki don yaki da ta'addanci, kiri da muzu ta tura jiragen sama wajen jejjefa boma-bomai a kan wata ma'aikatar hada magungunan sha a arewancin birnin Khartoum, bayan haka ta yi nufin neman samun ikon jagorancin harkokin kiyaye zaman lafiya a Darfur. A ran 29 ga watan Mayu na shekarar bara, Bush, shugaban kasar Amurka ya sanar da cewa, kasar Amurka za ta dauki sabbin matakai wajen kakkabawa kasar Sudan takunkumi, bayan da ta dade tana kakabawa kasar takunkumi. Duk wadannan matakai da kasar Amurka ta dauka sun gamu da adawa mai zafi daga wajen jama'ar kasar Sudan. Jama'ar Sudan sun sha yin zanga-zanga don yin adawa da takunkumi da kasar Amurka ta kakabawa kasar Sudan da katsalandan da ta yi wa harkokin gida na kasar Sudan. Jami'an gwamnatin kasar Sudan sun sha jaddada cewa, matakin da Bush ya sanar wajen kakabawa kasar Sudan takunkumi wani irin danyen aiki ne, yayin da halin da ake ciki a Darfur ya fara samun kyautatuwa, kasar Amurka ta tsaida kuduri a kan kara kakabawa kasar Sudan takunkumi, wannan aiki ne da aka yi na lalata zaman lafiya a yankin Darfur, ko kusa, gwamnatin kasar Sudan ba za ta durkusa a gaban matsin da Amurka ke yi mata ba.

1 2