Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-01 19:12:37    
Wurin yawon shakatawa na Potatso a lardin Yunnan

cri

Bayan sauka a tabkin Bitahai, mutane suna iya tukin kwale-kwale a cikin tabkin domin kallon kyan karkara da ke kewayen tabkin. Furannin azalea masu yawa suna girma sosai a kewayen tabkin Bitahai. Bayan ranar 5 ga watan Mayu na ko wace shekara bisa kalandar kasar Sin ta gargajiya, wadannan furanni sun yi toho kwarai. An ce, wasu kifaye su kan ci kunnen furannin da suka fado a kusa da bankin tabkin. Saboda yana kasancewa da guba kadan a cikin irin wannan fure, shi ya sa bayan da kifaye suka ci, su kan suma har awoyi 1 zuwa 2, su kan taso zuwa fuskar ruwa sai ka ce su ne bugaggu. Wannan na da matukar ban mamaki.

Almarar gargajiya mai ban mamaki da muhallin halittu da ake kiyaye shi yadda ya kamata sun bai wa mutanen da ke ziyara a wajen damar fahimtar kyan ganin halitta a cikin manyan tsaukuna a yankin da aka fi samun 'yan kabilar Zang. Malam Chen Lingfeng, wanda ya zo daga lardin Zhejiang, bayan da ya kammala ziyararsa a wajen, ya ce,

'Wannan wurin yawon shakatawa yana da kyau. Ina iya ganin kyawawan tabkuna da ruwa da kuma manyan tsaunuka, kuma an yi tsit a wajen. Kyan karkara a wajen ya sha bamban da na birane.'

A idon mazaunan birane, ko shakka babu wurin yawon shakatawa na Potatso wani wuri ne mai kyau wajen fahimtar kyan karkara na halitta da kuma saki jiki. A wajen, ba kawai sun iya kusantar da kansu a muhalli ba, har ma sun iya kara saninsu kan al'adun gargajiya na kabilar Zang. Akwai kauyuka 2 na 'yan kabilar Zang a wannan wurin yawon shakatawa. A kan hanyarku ta komawa gida, in kuna da lokaci, kuna iya ziyartar wadannan kauyuka.

Masu sauraro, Wurin yawon shakatawa na Potatso ya bai muku damar more ido da tabkuna da manyan tsaunuka da gandun daji a tuddai da ziyarar kauyukan 'yan kabilar Zang da gidajensu, da numfashin iska mai kyau da dandana namun shanun yak da kuma shan shayi irin na kabilar Zang, ya yi maraba da ku domin fahimtar kyan ganin halitta.


1 2