Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2008-01-01 19:12:37    
Wurin yawon shakatawa na Potatso a lardin Yunnan

cri

Wurin yawon shakatawa na Potatso na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin wurin yawon shakatawa na kasar Sin ne na farko, yana cikin gundumar Shangri-la na lardin Yunnan, shi ne wani kashi na shahararren wurin da ake samun kayayyakin tarihi na halitta na kasa da kasa, wato wurin da ake iya ganin kogunan Jingshanjiang da Lancangjia da kuma Nujiang suka gangara tare. A idon mutane, ya iya nuna ainihin kyaun ganin yankin Shangri-la. Fadin dukkan wannan wurin yawon shakatawa na matsayin kasar Sin ya kai kusan murabba'in kilomita dubu 2. Akwai tabkuna masu tsabta a kan tuddai da gandun daji da ba a iya ganin iyakarsa ba da filayen ciyayi masu fadi da kuma dabbobi da tsire-tsire da ba a iya kidaya yawansu ba.

Tabkin Shuduhu da tabkin Bitahai wuraren yawon shakatawa guda 2 ne masu muhimmanci da ake bude wa masu yawon shakatawa a cikin wurin yawon shakatawa na Potatso. In wani ya tsaya a bankin tabkin Shuduhu, nan da nan kyan karkara da ke gabansa ya kan burge shi. Shudin sararin sama da fararen gajimare da bishiyoyi masu launuka daban daban da kuma ruwan tabkin da ake iya ganin kyawawan manyan tsaunuka da sararin sama a ciki su kan sanya mutane su yi kama da shiga wani zane. Filayen ciyayi da ke bankin ruwan tabkin filin ciyayi ne da ya shahara a yankin kabilar Zang, in ji madam Dawazhuoma, mai jagorantar masu yawon shakatawa, 'yar kabilar Zang na wurin. Ta kuma kara da cewa,

'A bakin 'yan kabilar Zang, ma'anar Shudu ita ce wurin da cuku ya yi karfi kamar dutse. Wannan wuri wani makiyaya ne da 'yan kabilar Zang su kan kiwo dabbobin gida a lokacin zafi. Tun daga watan Mayu zuwa na Oktoba. 'yan kabilar Zang su kan yi kiwon shanun yak a makiyayan.'

A lokacin da wani ya ke tafiya a kan hanyar katako da aka shimfida a bankin tabkin Shuduhu, ruwa yana gangara a karkashin kafarsa. Ruwan da aka samu a tuddai ya yi wa tsire-tsire ban ruwa a wajen. Bayan da suka yi yawo a kewayen tabkin Shuduhu, mutane suna iya zuwa dakin cin abinci a wannan wurin yawon shakatawa domin huta kadan. An gina dakin cin abinci da katako bisa manyan tsaunuka. A gaban wannan gini, akwai wani gurbi da ya bullo saboda narkewar kankara mai laushi. Baya ga kallon ni'imtattun wurare, mutane sun iya dandana abinci mai dadin ci. Malam Lv Gang, kukun wannan dakin cin abinci ya yi karin bayani cewa,

'Mun dogara da namun shanun yak domin samar da abinci. Wurin nan wuri ne da aka fi samun 'yan kabilar Zang. 'Yan kabilar Zang sun dogara da cin naman shanun yak. Ban da wannan kuma, muna samar da abinci da wasu laiman kwadi, a ciki har da wasu masu daraja.'

An kaddamar da wannan dakin cin abinci a watan Agusta na shekarar 2006, wanda kuma dakin cin abinci ne kacal a wannan wurin yawon shakatawa. A kan yi jigilar dukkan shara daga dakin cin abincin cikin mota. Bayan da aka like su yadda ya kamata a kan binne su a karkashin kasa da zurfi a waje da wannan wurin yawon shakatawa.

Bayan cin abinci, mutane sun iya zuwa tabkin Bitahai cikin mota. Ta tagogin motar, suna iya ganin dimbin tsire-tsire masu launin kore da kuma wasu shanun yak da su kan bullo a tsakanin dogayen tsoffin itatuwa, wadanda gashinsu ke walkiya sosai a karkashin hasken rana.

1 2