Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-28 15:25:48    
Birnin Guangzhou na kasar Sin

cri

A hakika, birnin Guangzhou na da wani suna na daban, wato birni na raguna, game da wannan suna, akwai wata shahararriyar tatsuniya. An ce, a lokacin daular Zhou, wata rana, wasu kyawawan gajimare biyar na kusantar birnin Guangzhou daga tekun kudu, kuma a kan gajimaren, akwai mala'iku biyar da ke kan raguna biyar, sa'an nan, mala'ikun sun sauka a birnin Guangzhou tare da karan shinkafa, kuma sun bayar da kararen shinkafa ga mazaunan wurin, don yi musu fatan alheri na samun girbi mai kyau, kuma ragunan nan biyar an bar su sun zama duwatsu a birnin Guangzhou.

Birnin Guangzhou yana da dadadden tarihi har na tsawon shekaru fiye da 2,200. A birnin Guangzhou akwai wuraren tarihi masu yawa, wadanda yawansu ya kai har 219. Bayan haka, al'adu na musamman na jama'ar Guangzhou sun kuma burge ni sosai, misali wasan kwaikwayo na gargajiya na Guangzhou da kide-kide na Guangdong da zane-zanenta duk sun shahara a nan kasar Sin, har ma a duniya baki daya. Bayan haka, abinci na wurin ma sun yi suna sosai sabo da dadinsu, har ma sun zama daya daga cikin manyan hanyoyin dafa abinci guda takwas na kasar Sin. Sabo da haka, a nan kasar Sin, ana cewa, "abinci sai a birnin Guangzhou."

Ban da wadannan, Guangzhou ya shahara a duniya musamman sabo da bikin nune-nune kayayyakin shigi da fici na kasar Sin da ake gudanarwa a nan birnin Guangzhou sau biyu a kowace shekara. An fara gudanar da bikin ne daga shekarar 1957, kuma yanzu bikin ya riga ya zama wani gaggarumin bikin ciniki da ya fi tsawon tarihi da girma da nuna kayayyaki iri iri da kuma samun halartar baki.

To, Sanusi da dai sauran masu sauraronmu, idan wata rana kun sami damar zuwa nan kasar Sin, kada ku wuce birnin Guangzhou.(Lubabatu)


1 2