Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-28 15:25:48    
Birnin Guangzhou na kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Sanusi Isah Dankaba, mai sauraronmu da ya zo daga birnin Keffi, jihar Nasarawa, tarayyar Nijeriya. Kwanan baya, malamin ya rubuto mana cewa, shin ko birnin Guangzhou yana daya daga cikin manyan birane na kasar Sin? Ina neman cikakken tarihin birnin Guangzhou, babban birnin lardin Guangdong na kudancin kasar Sin?

To, Sanusi, gaskiyarka, birnin Guangzhou na daya daga cikin manyan biranen kasar Sin, kuma ya kasance babban birni na lardin Guangdong da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Kasancewar birnin a mashigin teku na kudu, yana fuskantar Hongkong da Macao, har ma ana kiransa kofar kasar Sin a kudu.

Fadin birnin Guangzhou ya kai muraba'in kilomita 7434.4, kuma yawan mazaunan birnin ya wuce miliyan 10. Yanayin Guangzhou yana da kyau, ba zafi sosai a lokacin zafi, a lokacin dari kuma, ba sanyi sosai, kuma ana samun ruwan sama da yawa a birnin, sabo da haka, ana iya ganin furanni ko ina, har ya zama wani muhimmin wuri na fitar da furanni a kasar Sin, har ma yana fitar da furanninsa zuwa kasashen waje. Ban da furanni, Guangzhou yana kuma shahara ne da 'ya'yan itatuwansa, har ma ana masa kirari "gari ne na 'ya'yan itatuwa", muhimman 'ya'yan itatuwan da aka samu a birnin su ne lychee da ayaba da abarba da gwanda da dai sauransu. Bayan haka, birnin Guangzhou yana kuma da dimbin ni'imtattun wuraren shakatawa, wadanda suka wuce 100.


1 2