Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-27 15:42:42    
An nuna wasannin kundunbala na gida na da na waje a Wuqiao

cri

Mr Katay Santos shi ne dan wasan kundunbala na kasar Venezuila. Don kara daga matsayinsa wajen fasahar nuna wasannin kundunbala, sai musamman ne ya shiga makarantar koyar da wasannin kundunbala na kasa da kasa na Wuwiao don koyon fasahar nuna wasannin kundunbala, ya bayyana cewa, na sauka Wuqiao cikin watanni hudu ke nan daga kasar Venezuila, ina dalilin da ya sa na sauka Wuqiao , shi ne saboda fasahar nuna wasannin kundunbala ta kasar Sin na da kyau sosai, na yi farin ciki da zuwan kasar Sin, wasan da nake koyo shi ne wasan jirgar jiki a kan igiya da kujeru.

An kafa makarantar koyar da fasahar wasannin kundunbala ta Wuqiao a shekarar 1983, Ban da dalibai 'yan asalin kasar Sin, sai kuma akwai daliban da suka zo daga kasashen waje da yawa. Daga shekarar 2002, gwamnatin kasar Sin ta soma samar da taimakon kudi ga daliban da suka zo Wuqiao don koyon fasahar wasannin kundunbala daga kasashen waje, kuma kowane dalibi zai iya koyon fasahar cikin shekara daya. Yanzu, da akwai daliban kasashen waje 24 da suke yin karatu a nan, daga cikinsu, wanda ke mafi karami shekarunsa ya kai 8 da haihuwa, amma wanda ke mafi girma shekarunsa ya kai 20 da wani abu, dukkansu suna da sha'awa sosai ga wasannin kundunbala. Shugaban makarantar ya bayyana cewa, yawan daliban kasashen waje da makarantar ta horar da su ya kai 150 ko fiye.

Tun daga shekarar 1956 har zuwa yanzu, kasar Sin ta yi ta samun sakamako mai kyau wajen gasar wasannin kundunbala a kasa da kasa, a cikin shekaru kusan 20 da suka wuce, kasar Sin tana ta kara kago sabbin abubuwa da samun bunkasuwa wajen fasahar wasannin kundunbala, yawan mindar zinariya da ta samu a gasar da aka yi a kasa da kasa ya wuce dari .Wani dan wasan kundunbala Mr Liang Zhen ya bayyana cewa, yana kaunar wasannin kundunbala, kuma yana son nuna wasan kundunbala a wurare daban daban, ya ce, na taba tafi kasar Malasiya da Korea ta Kudu , a manyan biranensu , na nuna wasannin kundunbala iri iri, kuma na sami karbuwa sosai daga wajen 'yan kallo.

Wang Baohe shi ne mai gadon fasahar wasan kundunbala na Wuqiao, ya bayyana cewa, muhimman halayen musamman na nuna wasannin kundunbala na zamani aru aru na kasar Sin su ne ba su sami damuwa saboda rashin wurare masu fadi ko masu kyau ba, kuma ba a yi amfani da kayayyakin wasa, ana iya nuna wasannin a ko'ina, bai kamata ba mu rasa wasannin gargajiya na zamani aru aru na kasar Sin , dana yana koyon fasahar wasan, dalibanmu ma suna koyon fasahar, za mu yada fasahar daga zuri'a zuwa zuri'a.(Halima)


1 2