Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-27 15:42:42    
An nuna wasannin kundunbala na gida na da na waje a Wuqiao

cri

Kwanan baya, a birnin Shijiazhuang na lardin Hebai da ke arewacin kasar Sin, an yi bikin rufe wasannin kundunbala na kasa da kasa na kasar Sin a karo na 11. Tun daga shekarar 1987 har zuwa yanzu, bikin nuna fasahar wasannin kundunbala na kasa da kasa na birnin Wuqiao ya riga ya zama daya daga cikin gasar wasannin kundunbala iri guda uku na duniya. An nuna fasahar wasannin kundunbala a dakalin daya na Wuqiao , wannan ya zama kasaitaccen al'amarin da aka yi a shekarar da muke ciki a rukunin wasannin kundunbala na duniya.

An soma yin wasannin kundunbala a daular Han a kasar Sin kafin shekaru fiye da dubu 2 da suka wuce. Bayanin da aka samu bayan binciken da aka yi kan kayayyakin tarihi na zamani aru aru da sauran bayanan tarihi sun bayyana cewa, a zamani aru aru, wasan kundunbala yana daya daga wasannin da ke samar da nishadi ga jama'ar farar hula wadanda suke iya samun damar kallonsa a yau da kullum. A filayen da ke waje da dakuna, 'yan wasan kundunbala sun nuna wasanni iri iri masu ban mamaki sosai ta hanyar yin amfani da sandan katako da kwanuka da irin makamantansu da wuka da adda da baka da kibau da sauran kayayyaki.

Wuqiao da ke kudancin lardin Hebai na kasar Sin shi ne wani kauyen da ake kwarewa a fannin fasahar wasannin kundunbala, inda aka samu kwararrun wasannin kundunbala da shahararrun wasannin kundunbala da yawa. Yanzu, a kauyen Wuqiao, ba ma kawai an kafa makarantun koyar da ilmin wasannin kundunbala da kungiyoyin nuna wasannin kundunbala ba, hatta ma an gina lambun shan iska da ke da babban jigo dangane da wasannin kundunbala. A kowace shekara, masu yawon shakatawa na gida da na waje da yawa suna kai ziyara a nan, sa'anan kuma da akwai mutanen kasashen waje da yawa da suke zuwa nan don koyon fasahar kundunbala ta kasar Sin.


1 2