Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 15:50:29    
Rage kiba yadda ya kamata zai ba da taimako ga lafiyar dan Adam

cri

Manazarta na jami'ar Harvard da ta Stanford ta kasar Amurka sun ba da wani rahoto a kan mujallar ilmin kimiyya na yara ta kasar Amurka a 'yan kwanakin nan da suka gabata, cewa sun gano cewa, game da mutane da dimbin yawa, ba kawai cin abinci dan kadan ba shi ne zai rage kibar jiki, har ma zai kara nauyin jikin mutane. Manazarta sun yi amfani da shekaru uku wajen gudanar da bincike ga yara dubu 15 da shekarunsu ya kai 9 zuwa 17 da haihuwa. Kuma sakamakon binciken ya nuna cewa, game da mutanen da su kan yin amfani da hanyar cin abinci dan kadan domin neman rage kibar jiki, sun fi saukin samun karuwar nauyin jiki fiye da kima idan an kwatanta su da wadanda su kan ci abinci kamar yadda ya kamata, ban da wannan kuma sun fi saukin kamuwa da dabi'ar cin abinci ko shan abin sha da yawa.

Bugu da kari kuma manazarta na kasar Amurka sun gudanar da bincike kan mutanen da suka tsaya tsayin daka kan yin amfani da hanyar cin abinci dan kadan domin neman rage kibar jiki. Daga baya kuma sun gano cewa, ko da yake wadannan mutane suna iya rage kiba da yawanta ya kai kashi 5 zuwa kashi 10 cikin dari a jikinsu a cikin makwanni 4 zuwa 6, amma sannu a hankali kuma, nauyin jikin yawancinsu yana sake karuwa, har ma sun samu kiba mafi yawa idan an kwatanta da na lokacin da. Haka kuma manazarta na jami'ar California ta Amurka sun gano cewa, kullum mutanen da suke da nauyi sosai su kan fara rage yawan abincin da suka ci har sau da yawa a lokacin yarantakarsu.

Sabo da haka kwararrun Amurka suna ganin cewa, ko da yake mai yiyuwa ne mutane suna iya rage kibar jikinsu ta hanyar cin abinci dan kadan a cikin gajeren lokaci, amma ba a iya kiyaye irin wannan sakamako mai kyau cikin dogon lokaci ba. Shi ya sa kwararru sun ba da shawara cewa, idan mutane suna son kiyaye lafiyar jikinsu sosai, ya fi kyau su ci abinci kamar yadda ya kamata da kuma motsa jiki a kullum.

A kwanan nan, cibiyar kare hakkin masu kashe kudi ta kasar Jamus ta buga wata ka'idar rage kiba, inda ta nuna cewa, shan ruwa a kalla lita 2 a ko wace rana zai ba da taimako ga mutanen da suke da kiba fiye da kima wajen rage kiba a jiki.

Ban da wannan kuma ka'idar ta ba da shawara cewa, idan ba a son shan ruwa, to ana iya shan shayi ba tare da sukari ba, haka kuma ana iya hada ruwa da ruwan 'ya'yan itace tare a sha.

Amma ka'idar ta yi gargadin cewa, bai kamata a sha kofi da bakin shayi da dimbin yawa a ko wace rana ba, kuma ya fi kyau kada a sha giya a lokacin abincin dare. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da irin wadannan abinsha suna kunshe da calorie da yawa, kuma ba za su ba da taimako wajen rage kiba a jiki ba. Kande Gao)


1 2