Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 15:50:29    
Rage kiba yadda ya kamata zai ba da taimako ga lafiyar dan Adam

cri

Manazarta na kasar Birtaniya sun gano cewa, mutanen da su kan ji gajiya sosai wajen aiki sun fi saukin samun kiba fiye da kima, shi ya sa ya kamata mutane masu shan aiki sosai su sassauta gajiya da suke ji da kansu.

Ta yin nazari a fannin ilmin likitanci, an riga an gano cewa, irin wannan gajiya da a kan ji wajen aiki a dogon lokaci yana da nasaba da cututtukan zuciya da na sauye-sauyen halittu. Amma a cikin wannan nazarin da Eric Brenner da abokan aikinsa na kwalejin ilmin likitanci na jami'ar London ta kasar Birtaniya suka yi, sun gano cewa, idan gajiya da masu aikin yi suka ji ta karu, sai yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su za ta karu.

Manazarta sun gudanar da wani bincike na tsawon shekaru 19 ga maza 6895 da kuma mata 3413 wadanda shekarunsu ya kai 35 zuwa 55 da haihuwa. A cikin binciken, wadannan mutane sun gabatar da takardun tambayoyi game da gajiyar da su kan ji wajen aiki na lokaci-lokaci. Kuma sakamakon binciken ya bayyana cewa, game da wadanda suka amince da jin gajiya sosai wajen aiki a cikin takardun tambayoyi har a kalla sau uku, yiyuwar samun kiba fiye da kima gare su ta karu da kashi 73 cikin dari idan an kwatanta da wadanda ba su taba jin gajiyar aiki ba.

Sabo da haka Mr. Brenner yana ganin cewa, wannan sakamakon bincike ya samar da wata muhimmiyar shaida kan cewa, gajiya wajen aiki ita ce muhimmin dalilin da ke haddasa samun kiba fiye da kima.

Idan mutane sun yi kiba fiye da kima, to su kan nemi dabaru masu yawa domin neman rage kibar. To, masu sauraro, yanzu sai ku shakata kadan, daga baya kuma za mu gaya muku wasu dabarun rage kiba.

Kullum mutanen da suka samu kiba fiye da kima su kan zabi hanyar cin abinci dan kadan wajen rage kiba a jiki, amma kwararrun kasar Amurka sun yi gargadin cewa, dogara bisa cin abinci dan kadan ba zai iya rage kiba a jiki ba.


1 2