Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 15:47:50    
Gandun daji na Shennongjia shi ne baitulmalin koren tsire-tsire

cri

A farkon shekaru 1990, baya ga dora muhimmanci kan kiyaye gandun daji na Shennongjia, hukumar yankin Shennongjia ta kuma raya aikin yawon shakatara na muhalli yadda ya kamata. Bunkasuwar aikin yawon shakatawa ya daukaka ci gaban ayyukan da abin ya shafa. Mr. Li Shikai, wani mazaunin gandun dajin ya kaddamar da wani otel. Lokacin zafi lokaci ne da ya fi samun kudin shiga. A ko wace rana, ya kan yi dimbin ayyuka, amma yana farin ciki ya kan yi murmushi. Ya ce:

'Tun bayan da aka raya aikin yawon shakatawa na muhalli a gandun dajinmu na Shennongjia har zuwa yanzu, halin da ake ciki a garinmu ya sami kyautatuwa sannu a hankali. Yawan masu yawon shakatawa na ta karuwa a lokacin zafi, shi ya sa na sami rancen kudi domin kaddamar da wannan otel. Mun sami karin kudade a shekarun nan.'

Ko da yake ci gaban aikin yawon shakatawa ya daukaka karuwar kudin shigar mazaunan, amma karuwar yawan masu yawon shakatawa ta kawo wa muhallin halittu na wannan gandun daji matsin lamba. Shi ya sa a farkon shekarar 2006, a karo na farko ne aka dakatar da karbar masu yawon shakatawa a gandun daji na Shennongjia a cikin watanni 3. Ta haka, nemun daji da ke zama a wajen sun sami hutu, sun iya kyautata kansu. Sa'an nan kuma muhallin halittu ya sami ingantuwa yadda ya kamata.

Yanzu an kaddamar da shirin kiyaye bishiyoyi na gandun daji na Shennongjia. An hana sare bishiyoyi domin kiyaye wannan gandun daji. Don haka, an maido da kyakkyawan muhallin halittu a gandun dajin sannu sannu. Madam Jiang Lingling, wata ma'aikaciyar kiyaye bishiyoyi ta ce:

'Tun bayan da aka gudanar da shirin kiyaye bishiyoyi a shekarar 2000 har zuwa yanzu, ana iya ganin biran da gashinsu mai launin zinariya da awaki na daji a manyan tsaunuka. Ban da wannan kuma, manyan tsaunukan sun zama kore, an kuma tsabta koguna.'?Tasallah?


1 2