Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 15:47:50    
Gandun daji na Shennongjia shi ne baitulmalin koren tsire-tsire

cri

Gandun daji na Shennongjia da ke arewa maso yammacin lardin Hubei na tsakiyar kasar Sin gandun daji ne da ba a taba yin amfani da shi ba tukunna, inda aka sami tsire-tsire iri fiye da dubu 3 da dari 7 da kuma namun daji iri fiye da dubu 1. An mayar da shi tamkar sansanin kwayoyin halitta wato gene na dabbobi da tsire-tsire kacal da aka adana shi a yankin tsakiya na layin da ya zagaye duniya, wato yankin middle latitude.

Fadinsa ya wuce murabba'in kilomita dubu 3 da dari 2, bishiyoyi sun mamaye shi mai fadin kusan kashi 70 cikin kashi dari. Malam Lei Jinguang, shekarunsa ya yi kusan 70 da haihuwa. Ya fara aiki a gandun daji na Shennongjia a matsayin ma'aikacin yanka bishiyoyi a lokacin da shekarunsa ya kai 20 da haihuwa. Ya waiwayi abubwan da suka wakana a lokacin da ya zo gandun dajin. Ya ce:

'A lokacin, gandun daji na Shennongjia gandun daji ne da ba a yi amfani da shi ba tukuna. Shi ya sa akwai namun daji masu tarin yawa, kamar su roes da bears da leopards da dai makamantansu.'

An sami kyawawan manyan tsaunuka da kuma bishiyoyi masu tarin yawa a gandun daji na Shennongjia, shi ya sa an samu dimbin albarkatu ta fuskar yawon shakatawa. Bugu da kari kuma, cikakken tsarin halittu masu rai irin na gandun daji da ba a taba amfani da shi ba, da ire-iren halittu da kuma yanayi mai dadi sun sanya gandun daji na Shennongjia ya sami kyawawan sunaye da yawa, kamar su baitulmalin koren tsire-tsire da wurin nune-nunen tsire-tsire da dabbobi na ikon Allah.

Birin da gashinsa mai launin zinariya wato golden monkey a Turance na kasancewa tamkar mala'ika ce ta gandun daji na Shennongjia, haka kuma, shi wani irin dabba ce da ke dab da karewa a duniya. Ya kan fito da bukatun da da kyar a biya a fannin muhallin halittu. A shekarun nan, muhallin halittu na gandun daji na Shennongjia ya sami kyautatuwa a kwana a tashi, shi ya sa yawan irin wannan birai masu daraja ya karu zuwa 1200 ko fiye, a maimakon guda 600 ko fiye a da. Wadannan kyawawa birai suna matsayin abu mai ban mamaki a wannan ni'imtaccen wuri. A lokacin da ya ji kukan wadannan birai, Mr. Qian Yuankun, wani jami'in hukumar wurin ya yi zumudi sosai, ya ce:

'Wasu sun nuna damuwa cewa, biran da gashinsu mai launin zinariya, kuma suna dab da karewa ba su iya zama a gandun daji na Shennongjia ba, sa'an nan kuma, gandun daji na Shennongjia zai bace. Amma yanzu da karfin zuciya muka sanar da cewa, kasar Sin ta sami nasarar kiyaye gandun daji na Shennongjia. Kuma yawan birai masu launin zinariya na ta karuwa, suna fadada wuraren da suke zama. Bisa kiyayewar da kasar Sin ta yi masa yadda ya kamata, gandun daji na Shennongjia ya kara ba da haske. Nan gaba gandun daji na Shennongjia zai zama wuri mai kyakkyawan muhalli, inda 'yan Adam da muhalli ke zama tare cikin jituwa.'


1 2