Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 08:36:16    
Share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ya daukaka ci gaban sha'anin nakasassu na kasar Sin

cri

Don shirya gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 yadda ya kamata a Beijing, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya kafa kungiyar musamman ta kwararru domin kyautata na'urori marasa shinge a filayen wasa na gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Kungiyar kwararrun ta yi binciken musamman kan dukkan wadannan filayen wasa ta fuskar muhalli maras shinge, sun yi ta yin kwaskwarima da kyautata muhalli maras shinge. A watan Afrilu na wannan shekara, bayan da suka yi bincike, jami'an kwamitin wasan Olympic na nakasassu na duniya sun nuna matukar yabo kan muhalli maras shinge na gasar wasannin Olympic ta Beijing. A halin yanzu, a nan Beijing, baya ga filayen wasa, nakasassu sun iya samun sauki a zamansu na yau da kullum a dukkan fannoni.

Bunkasuwar sha'anin nakasassu ta kasar Sin ta sami babban yabo daga kasashen duniya. Majalisar Dinkin Duniya da hukumomin kasa da kasa da abin ya shafa sun bai wa kasar Sin lambobin yabo fiye da 10. Madam Tang ta kara da cewa, 'Mun yi imani da cewa, a karkashin shugabancin gwamnatinmu, tare kuma da cikakken goyon baya daga dukkan jama'ar kasar Sin, tabbas ne Beijing za ta nuna wa gamayyar kasashen duniya gasar wasannin Olympic ta nakasassu mai ban sha'awa, haka kuma, sha'anin nakasassu na kasar Sin zai sami babban ci gaba.'(Tasallah)


1 2