Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-26 08:36:16    
Share fagen gasar wasannin Olympic ta nakasassu ya daukaka ci gaban sha'anin nakasassu na kasar Sin

cri

Bayan gasar wasannin Olympic ta Beijing ta shekarar 2008, kasar Sin za ta yi gasar wasannin Olympic ta nakasassu. Wannan gasa na matsayin wani shagali ga 'yan wasa nakasassu na duk duniya. Domin maraba da wannan shagali, kwamitin shirya gasar wasannin Olympic ta Beijing ya gabatar da wata wakar musamman mai suna 'Everyone is No.1', wato kowa da kowa na matsayi na farko, inda aka bayyana tunani na cewa, ko wane dan wasa nakasasshe ya sami damar zama zakara. Domin share fagen gasar wasannin Olympic ta Beijing, dimbin nakasassu na kasar Sin ba kawai sun sami damar zama zakara a kofar gidansu, wato a mahaifarsu ta kasar Sin ba, har ma sun kara samun sauki da kuma jin dadin zamansu.

Huang Jianbin, dan wasa ne da ya fito daga kungiyar wasan kwallon kwando kan keken hannu ta Beijing. A lokacin da muke ganinsa, yana samun horo a tsanake tare da abokan kungiyarsa a cibiyar horar da nakasassu a fannonin wasannin motsa jiki da fasahar sana'a ta Beijing. Malam Huang ya gaya mana cewa, dukkan kungiyarsa na zama a cibiyar. Baya ga samun horo, su kan ji dadin hutunsu a sabon dakin karatu da babban zauren ba da hidima. Ya ce, 'Mu kan sami horo na tsawon awoyi 2 da safe, haka kuma, wasu 2 da yamma. Galibin mu kan ci abinci da zama a wannan cibiya. Dakunan kwana na 'yan wasa na ba yabo ba fallasa. Abincin da mu kan ci abinci ne na musamman da ake samar mana. A galibi dai, mu kan ci abinci iri 6 ko 7. Abincin na da dadin ci.'

Share fagen gasar wasannin Olympic ta shekarar 2008 ya daukaka saurin bunkasuwar sha'anin wasannin motsa jiki na nakasassu na kasar Sin. A cikin shekaru da dama da suka wuce, baya ga wani guda a Beijing, gwamnatin Sin ta kafa sansanoni 18 na matsayin lardi domin horar da nakasassu ta fuskar wasanni. An ce, yanzu wasannin motsa jiki na bazuwa a tsakanin fararen hula nakasassu a kasar Sin, yawan wadanda suka nakasa a fannoni daban daban, sun kuma shiga gasannin wasan nakasassu na matsayin da ke sama da gundumomi ya wuce miliyan 2. A watan Oktoba na wannan shekara, kasar Sin ta sami nasarar shirya gasar wasannin Olympic ta musamman ta lokacin zafi ta kasa da kasa a birnin Shanghai, wadda ta sa kaimi kan ci gaban sha'anin nakasassu a kwakwalwa ta kasar Sin.

Bugu da kari kuma, gwamnatin Sin ta bai wa nakasassu ingantattun hidimomin kiwon lafiya da warkar da su da kuma horar da su a fannoni daban daban. Madam Tang Xiaoquan, shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin nakasassu ta kasar Sin ta gaya mana cewa, yanzu nakasassu fiye da miliyan 13 suna cin gajiyar tsarin warkar da su da kuma horar da su. Sa'an nan kuma, yawan yara nakasassu da suka shiga makaranta ya kara karuwa. An kafa makarantun musamman guda 1648 a duk kasar Sin domin fadakar da nakasassu. Matsakaicin yawan yaran da suka nakasa a ido da kunna da kwakwalwa, sun kuma shiga makaranta ya kai kashi 80 cikin kashi dari. Kazalika kuma, yawan nakasassun da suka sami aikin yi ya karu ba tare da tangarda ba. A yankunan karkara kuwa, nakasassu kimanin miliyan 10 suna da isasshen abinci da tufafi.

Malam Sha Chengshen, mataimakin shugaban hadaddiyar kungiyar kula da harkokin nakasassu ta Beijing ya ce, 'Warkar da nakasassu na da muhimmanci sosai. Shiga gasar wasannin Olympic ya iya nuna kyakkyawan ra'ayinsu a fannin wasanni kawai. Horar da su a fannin sana'o'i ya fi nuna muhimmanci a a gare su a zahiri, ta haka za a aza musu harsashe mai inganci wajen samun aikin yi. Nakasassu suna da irin wannan bukata, suna kuma zura ido kan a biya bukatunsu.'


1 2