Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-25 15:39:38    
Cibiyar harkokin al'adu da wasannin motsa jiki ta Wukesong

cri

Yanzu a nan Beijing, a gefen hanyar Fuxinglu ta arewa, wadda ke matsayin bangaren titin Changanjie da aka tsawaita shi zuwa yamma, a tsakanin hanya ta 3 da ta 4 da suka zagaya Beijing, ana dakufa kan wata cibiyar wasannin motsa jiki ta zamani, wato cibiyar harkokin al'adu da wasannin motsa jiki ta Wukesong. Jimlar fadin wannan cibiya ta zamani ta kai kadada 52 gaba daya, fadin gine-gine ya kai misalin murabba'in mita dubu 350. Ta hada da dakin wasa na Wukesong da filin wasan kwallon gora na Wukesong da gine-ginen ba da hidimar al'adu da wasanni da kuma al'umma da kuma wani babban filin nishadi na harkokin al'adu.

A cikin wadannan gine-gine, filin wasan kwallon gora na Wukesong filin wasa ne da za a yi amfani da shi domin shirya gasannin wasan kwallon gora a gun taron wasannin Olympic a shekara mai zuwa. Sa'an nan kuma, dakin wasa na Wukesong zai kasance dakin wasan kwallon kwado a gun taron wasannin Olympic na Beijing.

An sha warware matsaloli da yawa wajen tabbatar da shirin karshe na zayyana dakin wasa na Wukesong.

A cikin dukkan shirye-shiryen zayyana da aka tattara daga duk duniya a shekarar 2002, shirye-shiryen da kamfannonin zayyana guda 2 na kasashen Amurka da Switzerland suka tsara sun shiga zagaye na karshe. Bayan da kwararru suka ci gaba da yin tattaunawa a kansu, a karshe dai, sun zabi shirin da masu zayyana na kasar Switzerland suka tsara.

Amma duk da haka, bayan da kwararrun kasar Sin suka yi nazari a tsanake, sun gabatar da wasu matsaloli game da wannan shiri ta fuskar tsaron kai da fasaha. Ban da wannan kuma, bisa shirin da aka tsara a da, za a hada manyan allunan lantarki da ke nuna yadda wasanni ke gudana a kan bangwaye 4 a waje da filin wasan kwallon kwando. Amma wannan zai kashe kudi da yawa fiye da kima, sa'an nan kuma, a kewayen wadannan manyan allunan lantarki akwai unguwannin mazauna, irin wannan zayyana zai kawo illa ga zaman rayuwar mazaunan wurin, shi ya sa, a karshe dai, kwararrun kasar Sin sun tsai da kudurin ci gaba da hada wani allon lantarki, a maimakon duka. Bayan da aka yi kwaskwarima kan wannan shiri, za a kafa shiyyar kasuwanci mai fadin murabba'in dubu 100 a waje da filin wasan. Dakin wasan kwallon kwando na kasar zai ci gaba da kasancewa a matsayin wani gini, wanda ba a yi gyare-gyare kan siffarsa ba. amma an daga wurin da za a yi gasa da mita 7.8, haka kuma, an daga mashiga dakin na 'yan kallo zuwa doron kasa.


1 2