Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-24 16:45:44    
Ana shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta hanya mai sarkakkiya

cri

Na biyu, game da maganar Darfur, an sake fara yin shawarwarin shimfida zaman lafiya.

Ran 27 ga watan Oktoba, a karkashin jagorancin majalisar dinkin duniya da kungiyar gammayar Afirka, gwamantin kasar Sudan da kungiya mai adawa da gwamnatin ta Darfur sun yi shawarwarin shimfida zaman lafiya a birnin Surt da ke bankin teku na kasar Libya. Wannan shi ne na farko da gwamnatin kasar Sudan da dakaru mai adawa da gwanmatin Darfur sun yi shawarwarin zaman lafiya bayan sun daddale yarjejeniyar zaman lafiya a ran 5 ga watan Mayu na shekarar 2006 a Abuja, babban birnin kasar Nijeriya.

Gwamnatin kasar Sudan ta aika da wata kungiya hada da wakilai fiye da 30 zuwa birnin Surt, mataimakin shugaban jam'iyyar da ke kan karagar mulki ya jagoranci wannan kungiya. Kuma kungiyoyi 7 masu adawa da gwamnati sun halarci wannan shawarwarin zaman lafiya, amma kungiyar "Justice and Equality Movement" da sauran manyan kungiyoyi masu adawa da gwamnati ba su halarci wannan shawarwari ba.

Kafin sun yi shawarwarin zaman lafiya, an kai hari ga wani sansanin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarrayar Afirka da ke Darfur, kuma mutane 10 masu kiyaye zaman lafiya sun mutu, sauran mutane 7 sun jikkata. Wannan ya nuna cewa, ya zuwa yanzu, ana fuskantar da mawuyacin hali a yankin Darfur.

Gwamnatin kasar Sudan ta hadin kanta tare da MDD da kasashen duniya kan maganar Darfur. A ran 31 ga watan Yuli, kwamitin tsaro na MDD ya zartar da wani kuduri, ya bukaci a girke sojoji dubu 26 na kiyaye zaman lafiya hada da MDD da kungiyar tarrayar Afirka a yankin Darfur. A ran 24 ga watan Nuwamba, sojoji masu aikin injiniya 135 na kasar Sin na rundunar sosojin kiyaye zaman lafiya ta MDD da kungiyar tarrayar Afirka sun sauka a yankin Darfur, kuma sun zama sojojin rukuni na farko da MDD ta girke a yankin Darfur.


1 2