Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-24 16:45:44    
Ana shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta hanya mai sarkakkiya

cri

Jama'a masu sauraro. Yanzu lokaci ya yi da za mu gabatar muku da shirinmu na Afirka a yau. A cikin shirinmu na yau za mu yi muku bayani dangane da "ana shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta rikitaccen hanya".

Yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan yana kunshe da matakai biyu, da farko shi ne shimfida zaman lafiya tsakanin yankin arewa da kudancin kasar, na biyu shi ne shimfida zaman lafiya a yankin Darfur. Bayan kokarin da bangarorin da abin ya shafa suka yi, an riga an sami cigaba sosai kan wadannan matakai biyu, amma yana kasancewar matsala. Ko da yake akwai wuya, amma dole ne a shimfida zaman lafiya a kasar Sudan, kuma jama'ar kasar Sudan da kasashen duniya suna kara yin limani kan makomar zaman lafiya.

Da farko, ana fuskantar matsala wajen shimfida zaman lafiya tsakanin arewaci da kudancin kasar Sudan.

A ran 11 ga watan Oktoba na shekarar da muke ciki, ba zato ba tsamani kungiyar 'yantar da jama'ar Sudan da ke kudancin kasar Sudan ta janye daga cikin gwamnatin tsakiya, kuma ta gabatar da bukatu biyar ga gwamnati, kamar yin garanbawal cikin gwamnati, da warware matsalar ikon mallakar yankin Abyei, da sake girke sojoji na bangarorin biyu, da binciken yawan mutane, da kuma samun jituwar al'umma. Wannan shi ne hadarin siyasa mafi tsanani da gwamnatin kasar Sudan ta fuskanta tun bayan da aka kafa gwamnatin tarraya a shekarar 2005.

Bayan haka, shugaba Omer el-Bashir na kasar Sudan da Mr. Salva Kiir Mayardit, wato mataimakinsa na farko kuma shugaban kunigyar 'yanttar da jama'ar Sudan sun yi shawarwari sau uku a jere, kuma a ran 2 ga watan Nuwamba, sun sanar da cewa, sun riga sun daidaita rikicin siyasa da kasar Sudan ke fuskata.

Amma, saboda rashin samun ra'ayi iri daya kan wasu manyan batutuwa, a ran 29 ga watan Nuwamba, Mr. el-Bashir da Mr. Kiir sun sake yi shawarwari, kuma sun sake tabbatar da ka'idar warware matsala ta hanyar yin shawarwari.

Ko da yake har zuwa yanzu, ba a warware wannan rikicin siyasa sosai ba, amma ana iya ganin cewa, bubu yiyuwa bangarorin biyu za su sake bude wuta ga juna ba. Ban da haka kuma, tun bayan da bangarorin biyu suka daddale yarjejeniyar zaman lafiya, jama'ar kasar Sudan sun samun zaman lafiya, kuma tattalin arzikin kasar Sudan yana samun cigaba sosai. Yanzu, jama'ar kasar Sudan ba su son yaki.


1 2