Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 17:14:30    
Tarihin kungiyar FAO

cri

Sakamakon karuwar bukatun abinci a duniya da kuma hauhawar farashin makamashi da sauye-sauyen yanayi da dai sauransu, ana ta kara fama da matsalar karancin abinci. An ce, hatsin da aka samu a shekarar da muke ciki na iya biyan bukatun jama'a a shekara mai zuwa ne kawai, wanda ke nufin cewa, ba za a iya kara ajiyar hatsi yadda ya kamata ba. Irin wannan halin da ake ciki na karancin samar da abinci zai iya haddasa illoli ga kasashe masu tasowa, musamman ma kasashen da ke fama da karancin abinci.

Bisa hasashen da kungiyar FAO ta yi, an ce, yanzu a duk fadin duniya, mutanen da yawansu ya kai miliyan 840 na fama da karancin abinci a kullum, kuma daga cikinsu, miliyan 800 a kasashe maso tasowa ne suke, kuma dalilin da ya sa kungiyar FAO ta zabi "ikon mallakar abinci" da ya zama take na ranar abinci ta duniya a wannan shekara shi ne, don yin kira ga gwamnatocin kasashe daban daban da su kara mai da hankulansu a kan wannan babban hakki na bil Adam, kuma su dauki hakikanan matakai, don kara kawo abinci, kuma su rarraba abinci kamar yadda ya kamata, su yi yaki da yunwa da rashin isashen abinci masu gina jiki.(Lubabatu)


1 2