Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 17:14:30    
Tarihin kungiyar FAO

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Zainab Abubakar, wadda ta zo daga birnin Lagos, tarayyar Nijeriya. Malama Zainab ta turo mana wata wasika a kwanan baya da ke cewa, ina so ku ba ni tarihin kungiyar FAO, yaushe ne aka kafa kungiyar, kuma wadanne harkoki ne take gudanarwa?

Kungiyar FAO, wato Food and Agriculture Organization of the United Nations, ko kuma kungiyar kula da abinci da noma ta MDD, ta kafu ne a ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 1945 a birnin Quebec na kasar Canada, kuma a watan Disamba na shekarar 1946, kungiyar ta zamanto wani sashe na musamman na MDD, kuma yanzu hedkwatarta tana birnin Rome na kasar Italiya.

Manufar kungiyar FAO ita ce inganta lafiyar jikin jama'a da kyautata zaman rayuwarsu da kara inganta aikin kawo abinci da rarraba su, da taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin duniya da kuma kare dan Adam daga yunwa. Harkokin da kungiyar ke gudanarwa suna shafar fannonin noma da dazuzzuka da kiwon dabbobi da kamun kifi da kimiyya da fasaha da dai sauransu. Tana tattara bayanan da ke shafar aikin kawo abinci da cinikinsu, sa'an nan tana yin nazari a kan bayanan da kuma yada su zuwa kasashe daban daban. Bayan haka, tana kuma ba da tallafi ga kasashe mambobinta a fannin fasahohi da kuma kalubalanci gamayyar kasa da kasa da su zuba jari a fannin aikin noma.

Ya zuwa watan Nuwamba na shekarar 2007, yawan mambobin kungiyar ya riga ya kai 192.

A yayin da ake fama da matsalar karancin abinci a shekarun 1970 a duk fadin duniya, don yin kira da a dora muhimmanci a kan ayyukan noma da kuma abinci, a gun babban taron kungiyar FAO a karo na 20 da aka kira a shekarar 1979, an yanke shawarar mayar da ranar kafuwar kungiyar a matsayin ranar abinci ta duniya, wato ranar 16 ga watan Oktoba na kowace shekara. Sabo da haka, ranar 16 ga watan Oktoba na shekarar 1981 ta zamanto ranar abinci ta duniya a karo na farko. Daga baya, a kowace shekara, kungiyar FAO tare kuma da mambobinta su kan gudanar da bukukuwa daban daban bisa wani take na musamman, kuma taken ranar a wannan shekara shi ne "ikon mallakar abinci".

1 2