Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 15:45:31    
Ziyarar da Qadhafi ya yi a kasashen Turai ta taimaka ga kyautata dangantakar da ke tsakanin Libiya da Turai

cri

Ban da wannan kuma, ziyarar da Mr. Qadhafi ya yi a wannan gami a Turai ta taimaka ga kasashen Turai da su yi kokarin shiga ayyukan bunkasa tattalin arziki na kasar Libiya. Sabo da tsawon lokacin da kasashen duniya suka sa wa Libiya har ya kai shekaru 10, shi ya sa tattalin arzikin kasar ta sha babbar hasara, kuma tana bukatar farfado da tattalin arzikinta cikin gaggawa, da kara saurin bunkasa zaman al'umman kasar. Libiya tana fatan ta hanyar mayar da dangantakar da ke tsakaninta da kasashen kungiyar EU don bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki tsakanin bangarorin 2, da samun goyon baya wajen kudi da fasaha, kuma za ta samu taimako daga wajen kasashen Turai domin kafa tashar ba da wutar lantarki da karfin nukiliya.

Ban da wannan kuma, a gun ziyarar da Mr. Qadhafi ya yi a Turai, shi ma ya dukufa kan hadin gwiwar da ke tsakanin kasarsa da kasahen da ke kewayen bahar Rum. Ya nanata cewa, ya kamata Turai da Afirka su dauki nauyi ga shiyyar Bahar Rum tare, sabo da shiyyar nan za ta zama muhiimin wurin da ya hada Turai da Afirka. Ya bayyana cewa, ba shakka shiyyar bahar Rum tana fuskantar kalubale mai tsanani, tana bukatar bangarori daban-daban da su yi hadin gwiwa wajen kiyaye muhalli da sauyin yanayi da yaki da ta'addanci da sauran fannoni, ta yadda za a samu nasara domin magance irin wadannan kalubale. (Umaru)


1 2