Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-20 15:45:31    
Ziyarar da Qadhafi ya yi a kasashen Turai ta taimaka ga kyautata dangantakar da ke tsakanin Libiya da Turai

cri

Daga ran 6 ga wannan wata, Mr. Muammar Al-Qadhafi, shugaban kasar Libiya ya shafe kwanaki 13 yana yin ziyara a kasashen Portugal da Faransa da kuma Spain, a ran 8 ga wata a birnin Lisbon kuma ya halarci taro a karo na 2 na shugabannin kungiyar tarayyar Turai wato EU da na kungiyar tarayyar Afirka wato AU. Manazarta sun bayyana cewa, ziyarar da Qadhafi ya yi a kasashen Turai ta taimaka ga mayar da dangantaka a tsakanin Libiya da Turai yadda ya kamata kuma daga duk fannoni bisa tushen aminci da girmama wa juna.

Bayan da gwamnatin Libiya ta yi shelar a watan Disamba na shekarar 2003 cewa, bisa radin kanta ne ta yi watsi da shirin bunkasa makaman kare dangi, kasashen duniya sun cire takunkumin da suka yi mata a kai a kai, ita ma ta fara yin kokarin mayar da dangantakar da ke tsakaninta da kasashen yamma, musamman ma a tsakaninta da kasashen Turai. A watan Yuli na wannan shekara, bayan da kungiyar EU da kasar Faransa suka yi aikin sulhu, kasar Libiya ta yarda da komar da masu aikin jiyya guda 6 na kasar Bulgariya wadanda aka tuhume su da laifin yada kwayoyin cutar kanjamau a birnin Benghazi. Daga baya kuma Libiya da kungiyar EU sun daddale wata yarjejeniyar hadin gwiwa da abokantaka daga duk fannoni a tsakaninsu, daga nan dangantakar da ke tsakaninsu ta shiga wani sabon matakin bunkasuwa.

A gun wannan ziyarar da Mr. Qadhafi ya yi a Turai, sarki Juan Carlos 1 na kasar Spain da shugaba Nicolas Sarkozy na kasar Faransa dukkansu sun nuna masa aminci. Mr. Carlos ya ce, ziyarar da Mr. Qadhafi ya yi a kasar Spain ta samar da wani sabon masomin bunkasa dangantakar da ke tsakanin kasashen 2 bisa harsashin aminci da girmama wa juna, tana da amfani ga yin hakikanin hadi gwiwa domin samun moriyar jama'ar kasashen 2 da fuskantar kalubale da ke gabansu. Mr. Sarkozy shi ma ya bayyana cewa, ya yi marara da kasar Libiya da ta koma zaman al'umman kasashen duniya. A lokacin ziyararsa Mr. Qadhafi shi kansa ma ya nanata cewa, ko a wajen dangantakar da ke tsakanin bangarori 2, ko kuma wajen nahiyar Afirka da ta Turai, yana son kara hadin gwiwa a tsakaninsa da shugabannin sabbin burata na Turai bisa tushen hangen gaba, amma ba ta hanyar tsayawa kan hanyoyin da aka bi a da ba.

1 2