Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-18 16:26:32    
Puzhehei, Aljannar da ke duniyarmu

cri

A shekarun baya, hukumar gundumar Qiubei na dora muhimmanci kan raya aikin yawon shakatawa, ta kuma kyautata ayyukan da ke shafar harkokin yawon shakatawa sannu a hankali. Masu yawon shakatawa da ke ziyara a shiyyar Puzhehei ba kawai sun iya kara fahimta kan al'adun gargajiya gaba da baya, da cin abincin da manoma su kan ci, da kuma ziyarar gidajen da 'yan kananan kabilu ke zama ba, har ma sun iya yada zango a otel-otel masu inganci da kuma zuwa wuraren nishadi. Bunkasuwar aikin yawon shakatawa ta bai wa masu yawon shakatawa sauki, haka kuma, ta daukaka yalwatuwar tattalin arzikin wurin. Malam Bai Guangfu, wani jami'in hukumar gundumar Qiubei, ya gaya mana cewa:

'Hukumarmu ta gundumar Qiubei ta mayar da aikin yawon shakatawa a matsayin ginshikin gundumarmu a fannin samun bunkasuwa. Ci gaban aikin yawon shakatawa ya ba da babban tasiri kan ciyar da tattalin arziki da zaman al'ummar kasa na Qiubei gaba, haka kuma, ya bai wa mazaunan yankuna da ke makwabtaka da Qiubei taimako wajen kara samun kudin shiga, musamman ma yin zama a iyalan mazaunan yankunan karkara da kuma bunkasa kauyuka sun sami ci gaban da suka faranta wa mutane rai.'

Kyawawan manyan duwatsu da kananan tabkuna da kyan karkara da kuma dubun dubatan furannin lotus da suka girma sosai a shiyyar Puzhehei, wane ne ba zai nuna sha'awa kan wadannan abubuwa ba? (Tasallah)


1 2