Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-18 16:26:32    
Puzhehei, Aljannar da ke duniyarmu

cri

Lardin Yunnan muhimmin lardi ne na kasar Sin a fannin yawon shakatawa. Dimbin mutane sun taba jin sunayen Dali da Lijiang da Shangri-la a wannan lardi. Yau ma bari mu kawo wa Puzhehei da ke gundumar Qiubei ta yankin Wenshan na lardin Yunnan ziyara, wanda wuri ne mai kyan gani, kuma mazaunan wurin na da kirki sosai.

Puzhehei suna ne da aka kira dimbin tabkuna masu nuna tsarin yanayin kasa na Karst. Tana da nisa kilomita 280 a tsakaninta da birnin Kunming, babban birnin lardin Yunnan. Ma'anar Puzhehei a bakin 'yan kabilar Yi mazaunan wurin ita ce wuri mai dimbin kifaye da jatan lande. A shiyyar Puzhehei, ruwa mai fadin kadada dubu 3 ko fiye na da tsabta sosai. Kananan tabkuna sun yi kama da lu'u'lu'un da aka hada su tare, suna kuma kewaye da manyan duwatsu. Ta haka, manyan duwatsu sun hada ruwa, ruwa mai tsabta na kewayen kwarran manyan duwatsun. Malam Zhao Wenliang, shugaban hukumar aikin yawon shakatawa ta gundumar Qiubei, ya takaita sigogin musamman na Puzhehei da cewa:

'Sigogin musamman na shiyyar yawon shakatawa ta Puzhehei su ne muna da garin da ake samun dimbin ruwa irin na kabilar Yi, da wurare masu damshi masu nuna tsarin yanayin kasa na Karst, da duniyar furannin lotus da kuma kyakkyawan lambun da ke kan ruwa.'

Malam Nie Wei, dan birnin Kunming, ya sha ziyarar Puzhehei, ya yaba wa wannan wuri da cewa:

'Wurin nan kyakkyawan wuri ne, inda akwai kyawawan manyan duwatsu da tabkuna da kuma kyan karkara na ikon Allah. Ba a gurbata su ba.'

Masu yawon shakatawa da suka kawo wa Pizhehei ziyara su kan shiga kwale-kwalen da mazaunan wurin suka tuka domin yin yawo a kan ruwan tabkunan. Irin wannan karamin kwale kan dauka mutane 7 ko 8 kawai. Jikinsa ba ya da zurfi, shi ya sa, masu yawon shakatawa sun iya yin wasa da ruwa a lokacin da suke cikin kwale-kwalen, sa'an nan kuma, sun iya more idanunsu da kyan karkara saboda an tuka kwale-kwalen sannu sannu.

Shiyyar Puzhehei ta fi kyan gani a lokacin zafi da kaka. Saboda ban da kyawawan manyan duwatsu da tabkuna, dimbin furannin lotus suna tohuwa sosai a lokacin. Ganyayen furannin lotus sun barbazu a kan ruwa, har ma ba a iya ganin iyakarsu ba. Mutane kan numfashin kamshin furannin saboda iska. Mutane na iya ganin ganyayen lotus da furanninsu a kusa da hannunsu a lokacin da suke cikin kwale-kwalen.

Masu ziyarar shiyyar Puzhehei suna son more idanunsu ta hanyar kallon kyan karkara tare da yin fadan wasa da juna da ruwa. Ko abokai ko kuma wadanda ba su san juna ba, sun yi amfani da kwanuka da bokitai da dai sauransu domin daukar ruwa. A kan yi fara'a da murna a ko ina a kan kananan tabkuna. Ko da yake mutane sun jiku, amma sun ji farin ciki a zukatansu.

A lokacin da suke yawo a shiyyar yawon shakatawa ta Puzhehei, masu yawon shakatawa kada su manta da kara fahimtarsu kan al'adun gargajiya da halin musamman na wurin. Shiyyar Puzhehei wuri ne da aka fi samun 'yan kabilar Yi, ban da wannan kuma, an tsugunad da 'yan kabilun Zhuang da Yao da Miao a wajen. 'Yan kananan kabilu suna zama tare cikin jituwa a shiyyar Puzhehei. Ko wace kabila na da al'adun gargajiya masu dogon tarihi da ke nuna sigar musamman tata.


1 2