Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-18 16:24:33    
Yawan mutanen da ke sha'awar koyon sinanci yana ta karuwa

cri

Malama Kerstin Storm ta ce yanzu jamusawa dake koyon sinanci sun karu.Yayin da ta shiga jami'a,dalibi daya kacal ke koyon sinanci a cikin aji daya,ga shi yanzu sun kai arba'in.

Ana koyar da Sinanci a sauran kasashen Turai.Alal misali da akwai mutane dubu talatin dake koyon sinanci a Faransa wadda ta kama gaba a fannin nan a Turai. Britaniya ta hada kanta da sassan da abin ya shafa na kasar Sin wajen shirya littattafan karatu a makarantun sakandare.A Rasha mutanen da ke koyon sinanci sun yi karanci,shi ya sa kamfanoni da ma'aikatar harkokin waje da sauran sassan gwamnati su kan yi takara domin samun kwararru masu jin harshen sinanci.

Mista Gaston Caperton,shugaban kwamitin kula da harkokin jami'o'I na Amurka ya ce wajen kashi daya daga cikin kashi uku na manyan makarantu na Amurka dake da kos na koyar da sinanci.manhajan koyar da sinanci da gwamnatin Sin da Amurka suka fitar cikin hadin kai sun shiga makarantun sakandare da firamare na Amurka ta hanyar internet.ya ce"muna nan muna dukufa wajen wani aikin musamman na koyar da sinanci a makarantun sakandare da firamare na Amurka ta yadda 'yan makaranta zasu kara ilimi game da kasar Sin.Mu ma muna so mu kafa wata gada ta ma'amala da cudanya tsakanin Amurka da kasar Sin."(Bilkisu)


1 2