Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-18 16:24:33    
Yawan mutanen da ke sha'awar koyon sinanci yana ta karuwa

cri

Sinanci wani harshe da mutane mafiya yawa ke amfani da shi a duniya. A cikin shekarun baya kasar Sin ta kara bude kofarta ga kasashen waje da kuma tattalin arzikinta na ta samun saurin cigaba,kasar Sin ta kara yin mu'amala da cudanya da sauran kasashen duniya a fannoni daban daban.A sa'I daya kuma mutanen kasar Sin dake dalibta da ciniki da yawon shakatawa a sauran kasashen duniya sai kara yawa suke cikin sauri.A kan matsayin kayan aiki na kara ilimi dangane da kasar Sin,gwamnatoci da hukumomin ilimi na kasashe da yawa sun dora muhimmanci kan harshen Sinanci.

Daga cikin mutane wadanda ke koyon sinanci,mutanen Vietnam da Thailand da Korea ta kudu da Japan da sauran kasashe makwabtan kasar Sin sun fi yawa.Dalili kuwa shi ne al'adun wadannan kasashe sun kusanci al'adun kasar Sin,na biyu mu'amala da suke yi da kasar Sin ta fi yawa.Sabili da haka mutane da yawa a wadannan kasashe suna koyon sinanci.

Mista Vu Minh Tuan,wani jami'in ma'aikatar ilimi da horo ta kasar Vietnam ya bayyana cewa matasa da yawa na Vietnam suna sha'awar koyon Sinanci.Ya ce "a halin yanzu 'yan makaranta na Vietnam suna kishin koyon Sinanci.Ban da jami'a da akwai cibiyoyi da yawa na koyar da sinanci,'yan makaranta su kan koyi sinanci bayan lokacin makaranta."

A zahiri ba a Vietnam kawai ba har ma a kudu maso gabashin Asiya haka al'amari yake.mutane na sha'awar koyon sinanci.A makarantun firamare da sakandare da yawa an samar da kos na koyon sinanci,har ma a wasu hukumomin ba da horo na zamantakewar al'umma.Bisa alkaluman da aka yi,an ce mutanen dake koyon sinanci a kudu maso gabashin Asiya sun kai kimanin miliyan daya da dubu dari shida.

A kasar Korea ta kudu da Japan dake Asiya ta gabas,mutanen da ke koyon sinanci kullum suna kara yawa,da akwai jami'o'i kimanin metan dake da kos na koyar da sinanci,an mai da sinanci batu na jarrabawa domin shiga jami'a.Da akwai mutane sama da miliyan biyu dake koyon sinanci a Japan,manyan makarntun sakandare dake da kos din koyon sinanci sun karu da ninki goma cikin shekaru 20 da suka shige.

Malama Kerstin Storm wata daliba ce ta jami'ar Minstel ta kasar Jamus ta koyi sinanci na tsawon shekaru hudu.Ga shi a yau tana yin magana da sinanci sosai.Ta gaya wa wakilin gidan rediyonmu cewa koyon sinanci zabi ne na idon basira. Ta ce "yanzu da akwai damar samun aikin yi da yawa a kasar Sin,kamfanonin da yawa na Jamus sun kafa sassansu a kasar Sin,huldar kasuwancin dake tsakanin Jamus da Sin ta kara karfi.shi ya sa a ganina koyon sinanci yana da amfani sosai gare ni domin samun aikin yi.


1 2