Mr. Ugwu ya gaya wa Tang Qiang, babban direktan kamfanin raya unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci, cewar tabbas ne za a gamu da matsaloli iri daban-dabam lokacin da ake raya unguwar. Ya riga ya nemi hukumomin gwamnati da abin ya shafa da su kara yin hadin gwiwa domin daidaita matsalolin da aka samu wajen shigar da injuna da na'urori da sauran kayayyaki da ma'aikata cikin unguwar.
Mr. Ugwu ya kara da cewa, jihar Ikko tana da sa'a domin tana da unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci. Ya yi imani cewa, tabbas ne za a samu muhimman sauye-sauye a unguwar. Sabo da haka, ya nemi gwamnatin jihar Ikko da ta kara zuba kudade kan ayyukan yau da kullum, kamar su hanyoyin mota da tashoshin ruwa a yankunan da ke makwabtaka da unguwar.
Jama'a masu sauraro, ya zuwa watan Yuli na shekarar 2007, masana'antun kasar Sin 3 sun riga sun sa hannu a kan yarjejeniya domin kafa sassansu a cikin unguwar. A waje daya kuma, sauran manyan masana'antu da kamfanonin kasar Sin da na kasashen duniya, ciki har da kamfanin Shell da kamfanin Total sun riga sun sa hannu a kan yarjejeniyar nuna sha'awarsu ta kafa sassansu a cikin unguwar. Bugu da kari kuma, sauran kamfanonin kasar Sin da na sauran kasashen duniya fiye da 100 sun bayyana fatansu na shiga unguwar. 1 2
|