Unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci tana tsibirin Lekki da take nesa da cibiyar birnin Ikko da kimanin kilomita 50. Fadin unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci da aka kebe ya kai murabba'in kilomita 165. Yanzu wannan unguwa tana daya daga cikin sabbin unguwoyin da suka fi samun bunkasuwa cikin sauri a kasar Nijeriya.
A shekara ta 2003 ce aka fara raya wannan unguwa. A karkashin goyon baya da gwamnatin kasar Nijeriya ta nuna musu, wasu kamfanonin kasar Sin, kamar su kamfanin Bei Ya da kamfanin CCECC da babban kamfanin gina ayyukan yau da kullum da ke da nasaba da hanyar dogo na kasar Sin sun zuba jari sun kafa wata kawance tare domin raya wannan unguwar Lekki. Bayan da aka raya ta a cikin shekaru 4 da suka wuce, yanzu za a iya ganin wasu halayen rinjaye a unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci.
Kasar Nijeriya kasa ce daga cikin mambobin da suke kulla "Yarjejeniyar Lome". A kasuwannin kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai, ana buga harajin kwastam ga kayayyaki kirar Nijeriya bisa sharuda masu gatanci, kuma ba a kayyade kaso ba. Sabo da haka, idan an kafa masana'antu a cikin unguwar, za a iya sasauta kiki-kakar cinikin waje a kasuwannin kasa da kasa. Bugu da kari kuma, wannan unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci za ta sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Nijeriya, kuma za ta iya samar da guraban aikin yi masu dimbin yawa. Mr. Tang Qiang, babban direktan kamfanin raya unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci ya ce, domin cigaban da kasar Sin ta samu a fannin tattalin arziki ya jawo hankulan mutane sosai, kasashen Afirka suna da sha'awa kan hanyoyin bunkasa tattalin arziki da kasar Sin take bi. Kasar Nijeriya ma tana fatan za a iya shigar da fasahohin raya tattalin arziki daga kasar Sin domin ciyar da tattalin arzikinta gaba.
A ran 10 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, gwamna Fashola na gwamnatin jihar Ikko ya shugabanci kwamishinonin hukumomin gwamnatin jihar da su yi rangadin aiki a unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci domin neman sanin yadda ake raya wannan unguwa. Lokacin da yake rangadin aiki a unguwar, Mr. Fashola ya nemi hukumomin gwamnatin jihar da sarkuna da su yi namijin kokarinsu wajen nuna goyon baya ga bunkasuwar unguwar. Ya zuwa yanzu bisa kokarin da bangarorin Sin da Nijeriya suka yi tare, an riga an kammala ayyukan shimfida wasu muhimman hanyoyin mota a cikin unguwar.
Haka kuma, a ran 30 ga watan Nuwamba na shekarar da muke ciki, Mr. Charles Ugwu, ministan kasuwancin kasar Nijeriya shi ma ya kai ziyara ga unguwar Lekki ta yin ciniki cikin 'yanci da ake gina shi cikin sauri. Mr. Ugwu ya yi murna sosai ga cigaban da aka samu wajen ayyukan gina wannan unguwa, da hanyoyin mota da aka shimfida a cikin unguwar. A waje daya kuma, Mr. Ugwu ya ce, gwamnatin tarayyar Nijeriya za ta ba da tabbaci ga ayyukan gina unguwar.
1 2
|