
Malam Cao Haizheng ya ci gaba da cewa, babban dalilin da ya sa aka iya ci gaba kamar haka a garin Manzhouli, shi ne domin matsayinsa mai rinjaye na yin cinikayya a tsakanin kasashen Sin da Rasha. Yanzu, yawan jiragen kasa dauke da gurbataccen man fetur da timban wadanda yawansu ya kai misalin 10, suna ta sauka a garin Manzhouli a ko wace rana, a sa'i daya jiragen kasa dauke da motoci da na'urori masu aiki da wutar lantarki da kayayyakin saka da kayayyakin lambu da 'ya'yan itatuwa da makamantansu suna ta zuwa kasar Rasha daga kasar Sin.
Malam Li Weihe, mataimakin shugaban hukumar kula da harkokin cinikin waje ta garin Manzhouli ya bayyana cewa, "yawancin abubuwan da ake jigilarsu ta hanyar jirgin kasa daga garinmu zuwa Rasha hajoji ne. Nauyin abubuwan nan ya kai tan miliyan 21 da dubu 710 a shekarar bara. Bisa shirin da muka tsara, nauyin abubuwan nan zai karu zuwa tan miliyan 24. Nauyin abubuwan da muka riga muka yi jigilarsu ya wuce tan miliyan 12 a farkon rabin shekarar nan, wato ke nan mun kammala sama da rabin aikinmu. "
Aiki mai kyau da hukumar kwastan ke yi a garin Manzhouli ya sami babban yabo daga wajen 'yan kasuwa na kasashen Sin da Rasha. Malam Zhang Tieqiang, dan kasuwa na kasar Sin wanda ke yin aikin gyara timban ya bayyana cewa, "da ya ke aikin da hukumar kwastan ke yi cikin sauri, mu kan yi tsimin kudin Sin Renminbi Yuan dubu 2 wato kimanin dalar Amurka 266 a kan ko wane kwantena." (Halilu) 1 2
|