Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-17 16:43:28    
Ana bunkasa harkokin ciniki tsakanin kasashen Sin da Rasha

cri

Gari mai suna Manzhouli yana arewacin jihar Mongoliya ta gida mai ikon aiwatar da harkokin kanta a kasar Sin, kuma yana kan bakin iyakar kasa a tsakanin kasashen Sin da Rasha. A cikin shekarun nan da suka wuce, bisa matsayinsa mai rinjaye, garin ya nuna himma sosai ga bunkasa harkokin ciniki a tsakanin Sin da Rasha, ta haka yanzu ya riga ya kasance a sahun gaba a kasar Sin wajen bunkasa harkokin tattalin arziki.

A garin Manzhouli na kasar Sin, a kan ga 'yan kasuwa na kasar Rasha na sayan kayayyakin kasar Sin a titunan kasuwanci inda mutane ke rididin kai da kawowa, suna tuntubar farashin kayayyakin musamman tufafi da kananan kayayyaki masu aiki da wutar lantarki da sauransu. Malam Vladislav wanda ya fito daga wurin Baykal na kasar Rasha ya nuna wa wakilinmu wandon da ya saya, ya ce, "na kan zo garin Manzhouli don sayen kayayyaki, garin Manzhouli wani gari ne mai kyaun gani sosai. Ina kaunarsa kwarai, kuma ina da abokai da yawa a cikin garin. Lalle, ina jin dadainsa ainun. A nan na sayi riga da wando da takalma da kuma teliho. Kayayyakin kasar Sin suna da inganci sosai kuma da raha."

Ban da irin wannan karamin cinikin da ake yi a garin Manzhouli, kuma an yi ta bunkasa harkokin cinikayyar waje a tsakaninsa da kasar Rasha a cikin shekarun nan da suka gabata. Malam Cao Haizheng, wani jami'in gwamnatin garin ya bayyana cewa, a da garinmu wata hanya ce da ake bi wajen jigilar kayayyaki a tsakanin kasashen Sin da Rasha, amma yanzu, garinmu shi ma ya fara bunkasa masana'antun gyaran kayayyaki bisa halin da ake ciki. Ya kara da cewa, "a shekarar bara, garinmu ya fara gyaran tumban da aka shigo da su daga kasar ketare. Yawan tumban da muke iya gyara su ya kai cubic mita miliyan 3 a shekara guda daya. Sa'an nan kuma muna gyaran kayayyakin lambun da ake fitarwa zuwa kasar Rasha. Yanzu, yawancin kayayyakin lambun da kasar Sin ke fitarwa zuwa kasar Rasha na garin Manzhouli ne. kazalika garinmu yana bunkasa masana'antun sarrafa kayayyakin bayan gida da injunan noma da kayayyakin gida masu aiki da wutar lantarki da sauransu wadanda ake fitar da su zuwa kasashen waje."

1 2