Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-14 15:27:26    
Manyan tsaunukan Yuntaishan da ke lardin Henan na kasar Sin

cri

A cikin shiyyar manyan tsaunukan Yuntaishan mai fadin daruruwan murabba'in kilomita, akwai yawan tsaunukan da suke hade da juna. Babban tsauni mafi tsayi a wajen shi ne babban tsaunin Zhuyufeng, tsayinsa ya wuce mita 1300. Yin watsal-watsal a lokacin hawan wannan babban tsauni ta dimbin matakai ya yi kama da yin yawo a tsakanin gajimare, gajimare kan tafiya a kusa da mutane. In an hango daga kololuwar babban tsaunin Zhuyufeng, sai ana iya ganin tekun gajimare, sai kololuwar manyan tsaunuka kawai kan bullo a cikin tekun gajimare, sai ka ce su ne feshin ruwa da ke kan teku.

Saboda shiyyar manyan tsaunukan Yuntaishan ta yi girma, shi ya sa masu yawon shakatawa kan dauke a kalla rabin awa domin ziyarar wurin yawon shakatawa daya, a takaice dai, awoyin da su kan kashe domin ziyara ba su kai 2 ko kuma 3 ba, sa'an nan kuma, ziyarar dukkan wannan shiyya kan bukatar karin tsawon lokaci. Don taimakawa masu yawon shakatawa a fannin yin tsimin kudi, hukumar kula da shiyyar manyan tsaunukan Yuntaishan ta aiwatar da tsarin amfani da tikitin shiga shiyyar na tsawon kwanaki 2.

Irin wannan tsarin ya sami amincewa daga masu yawon shakatawa saboda ya biya bukatunsu sosai, ya kuma ba su sauki da gatanci.

Ko da yake akwai dimbin wuraren yawon shakatawa a manyan tsaunukan Yuntaishan, amma dubban masu yawon shakatawa na gida da na waje da suka kawo nan ziyara a ko wace rana ba su dami bata hanya ba. A ko ina a wajen, masu yawon shakatawa baki na iya ganin allunan nuna hanya da na yin gargadi da na yin karin bayani kan wurin yawon shakatawa, wadanda aka yi amfani da Sinanci da Turanci da Japananci da harshen Korea domin bai wa dukkan masu yawon shakatawa na gida da na waje sauki. Malam Li Jie, shugaban hukumar kula da wannan shiyya, ya ce,

'Mun yi amfani da Sinanci da Turanci da Japananci da kuma harshen Korea a kan allunan nuna hanya masu adadin misalin kashi 70 cikin kashi dari a shiyyarmu. In masu yawon shakatawa baki sun bata hanya, ba su ga mai jagorantarsu ba, za su nemi kungiyarsu cikin sauri ta yin amfani da allunanmu.'

A zarihi hukumar kula da wannan shiyya tana daukar yawan matakai domin faranta wa masu yawon shakatawa rai da kuma sakin jikinsu. Malam Huang Weisen, dan kasar Malaysia, amma asalinsa kasar Sin, ya nuna gamsuwa sosai kan wadannan hidimomin da hukumar kula da shiyyar manyan tsaunukun Yuntaishan ke bayarwa domin mayar da mutane a gaban kome. Ya ce,

'Wannan shiyya na da kyan gani sosai, kuma tana da tsabta sosai. Mun yi farin ciki a lokacin da muke yawo a wajen. Hukumar wannan shiyya ta ba da hidimomi daga dukkan fannoni.'(Tasallah)


1 2