Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-14 15:27:26    
Manyan tsaunukan Yuntaishan da ke lardin Henan na kasar Sin

cri

Akwai kyawawan wuraren yawon shakatawa masu dimbin yawa a kasar Sin, shiyyar yawon shakatawa ta manyan tsaunukan Yuntaishan na daya daga cikinsu. Shiyyar yawon shakatawa ta manyan tsaunukan Yuntaishan na cikin gundumar Xiuwu ta birnin Jiaozuo na lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin, ita kuma wurin yawon shakatawa ce na nuna tsarin yanayin kasa a rukuni na farko da hukumar ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya wato UNESCO ta zaba daga duk duniya. Fadinta ya kai kusan murabba'in kilomita 200, inda marmaron ruwa da yawa suka bullo a tsakanin manyan tsaunuka.

A manyan tsaunukan Yuntaishan, ruwa na buya a tsakanin manyan tsaunukan, suna can suna jiran masu yawon shakatawa. Mutane kan siffanta ruwan da ke ko ina a wajen da cewar, in ka taka matakai 3, sai ka ga wani marmaron ruwa; in ka taka matakai 5, sai ka ga wata gangarar ruwa; bayan matakai 10 kuwa, ka iya ganin wani karamin tabki. In wani ya kai ziyara ga manyan tsaunukan Yuntaishan, to, ya fi kyau ya yi kwanaki da dama yana zama a otel-otel a cikin manyan tsaunukan, wadanda mazaunan wurin suka raya gidajensu zuwa irin wannan otel din musamman. Ko da yake ba a kayatar da su sosai ba, haka kuma kudin hayan daki na da araha, amma masu yawon shakatawa kan ji dadin zamansu a tsaunukan. Malam Wang Jianfeng ya sha kai wa manyan tsaunukan Yuntaishan ziyara, ya yi zama a cikin irin wadannan otel-otel din a ko wane karo. Ya ce,

'Na taba ziyara a manyan tsaunukan Yuntaishan sau biyu ko kuma uku. A ganina, yin zama a wadannan otel-otel yana da kyau sosai, sharuddan zama kuma suna da kyau, kudin hayan daki ba shi da tsada. Na gaya wa abokaina da yawa game da manyan tsaunukan Yuntaishan, dukkansu sun bayyana burinsu na ziyara a wajen.'


1 2