Mr Liu Binjie ya ci gaba da bayyana cewa, a wani fanni, wajen yaki da laifufukan satar fasahohin dabi, ya kamata a dogara bisa karfin shari'a da kuma dogara bisa aikin da hukumomin gwamnati suka yi wajen aiwatar da dokokin shari'a, amma a karshe dai in ana son daidaita matsalolin satar fasahohin dabi, to dole ne a dogara bisa karfin jama'a.
Saboda haka matakin kafa cibiyar yaki da laifufukan satar fasahohin dabi ya sami goyon baya da yabo daga wadanda suke da ikon wallafe-wallafe.
Mr Liu Binjie ya kuma bayyana cewa, dukkan mutane na kasar Sin ko na kasashen waje ko kungiyoyin jama'a ko a gida ko a waje, dukkansu suna iya samun lambar yabo bisa sakamakon ba da gudumuwa wajen gabatar da rahotannin tonon laifufukan satar fasahohin dabi, yawan kudin yabo zai kai kudin Sin Yuan dubu 100. (Halima) 1 2 3
|