Saboda haka babban kamfanin Xugong ya tsara manyan tsare-tsaren bunkasuwa a duniya. Da farko, ya gudanar da harkokinsa musamman a kasashe masu tasowa da kasashe da ke makwabtaka da kasar Sin, kana kuma zai sayar da injunansa a kasashe masu sukuni sannu a hankali. Bayan da ya shiga kasuwannin kudu maso gabashin Asiya da gabas ta tsakiya da arewancin Amurka yadda ya kamata, ya fara gudanar da harkokinsa a sabbin kasuwanni na Afrika da kudancin Amurka da kuma Turai. Yanzu, babban kamfanin Xugong ya riga ya sayar da injunan aikinsa zuwa kasashe da shiyyoyi sama da 80 na Afrika da gabas ta tsakiya da Turai da nahiyar Amurka ta arewa da ta kudu. Kamfaninsa kuma yana kara samun ci gaba wajen mayar da samfurin injunansa da ya zama shahararren samfuri a duniya.
Duk da haka babban kamfanin Xugong ya gano cewa, ya kasance da gibi a tsakaninsa da manyan kamfanonin kasa da kasa da suka shahara a duniya a fannonin kula da harkokin kamfani da nazarin sabbin injuna da sauransu. Malam Wang Min, shugaban kwamitin zartaswa na babban kamfanin ya bayyana cewa, "alal misali, kamfaninsa zai kara samun karfinsa na yin takara a kasuwannin duniya ta hanyar daga ingancin injunansa, amma ba ta hanyar sayar da injuna masu yawa kawai ba. Ta haka kamfaninsa zai iya kara samun kaso mai yawa na injunan da ake sayarwa a kasuwannin duniya, sa'an nan samfurin injunansa ma zai kara samun kwarjini daga wajen masaya na duniya."
Bayan haka Malam Wang Min ya ci gaba da cewa, wajibi ne, babban kamfanin Xugong ya kasance cikin shiri sosai don cim ma manufarsa game da samun kwarewa wajen yin takara a kasuwannin duniya. Ya ce, "wajibi ne, mu nace ga aiwatar da manufar yin kwaskwarima da bude wa kasashen waje kofa, mu yi amfani da sakamako da manyan kamfanonin duniya suka samu a fannin fasaha. Amma a yayin da muke yin haka, kamata ya yi, mu nace ga bin manufarmu, mu kara kwarewa wajen gudanar da harkokinmu cikin gashin kai, sa'an nan ba mu canja wannan matsayi ba. " (Halilu) 1 2
|