Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-10 16:01:33    
Babban kamfani mai suna Xugong na kasar Sin ke gudanar da harkokinsa a kasuwannin duniya

cri

An kafa babban kamfani mai suna Xugong a shekarar 1989 a birnin Xuzhou na lardin Jiangsu da ke a gabashin kasar Sin. Babban aikinsa shi ne kera injuna. A farkon lokacin kafuwarsa, yawan kudin shiga da ya samu ya kai kudin Sin Renminbi Yuan miliyan 300 kawai, amma ana kyautata zaton cewa, yawan kudin nan zai kai kudin Sin Yuan biliyan 30 a dukkan shekarar nan, wato ke nan zai yi ninki 100 bisa na shekarar da aka kafa ta. Ban da wannan kuma yawan kudin da take samu daga wajen sayar da injuna ga kasashen waje zai kai dalar Amurka miliyan 500 a shekarar nan. Yanzu babban kamfanin Xugong ya riga ya zama kamfani ne mafi girma da ke fitar da injuna a kasar Sin, haka kuma yana kokarin cim ma manufarsa don zaman wani kamfani da zai kware sosai wajen yin takara a kasuwannin sayar da injunan aiki a duniya.

Malam Wang Min, shugaban kwamitin gudanarwa na babban kamfanin Xugong yana ganin cewa, idan kamfaninsa ya yi fatan zai mayar da samfurin injunansa da ya zama samfuri da zai shahara a duniya, to, zai yi ta yin kokari har cikin dogon lokaci. Ya kara da cewa, "na farko, wajibi ne, injunan da kamfaninsa ke samarwa su iya biyan bukatun da ake yi a kasuwannin duniya. Sa'an nan kuma kamfanin ya kafa tsarinsa na samar da kayayyakin gyarawa da na ba da hidima ga masayan kasashen waje yadda ya kamata. Na biyu, ya kafa cibiyar nazarinsa a kasashen waje, ta yadda zai kasance cikin sahun gaba a duniya ta fuskar injunan aiki. Bayan haka, kamfaninsa zai iya fara gudanar da harkokinsa a kasuwannin duniya a lokacin da ya ga dama, sa'an nan zai yi ta yin kokari wajen mayar da samfurin injunansa don ya zama shahararren samfuri a duniya sannu a hankali."


1 2