Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-06 18:39:22    
An kafa kolejin watsa labarai ta Confucius ta farko a kasar Sin

cri

Yanzu da akwai kulob din masu sauraron rediyon kasar Sin da yawansu ya kai fiye da 3,000 wadanda ke kasance ko'ina na manyan nahiyoyi 5. Kolejin watsa labarai ta Conficius za ta zabi wasu masu kyau daga cikinsu don su kafa dakunan ba da darussan Confucius ta hanyar watsa labarai. Yanzu yawan irin wadannan dakuna ya kai 10 wadanda aka gina ko kuma ake ginawa, daga cikinsu har da dakin ba da darussan Confucius ta hanyar watsa labari da ke birnin Nairobi na kasar Kenya, da na hadaddiyar kungiyar sada zumunci tsakanin Japan da Sin da ke wata gundumar kasar Japan.

Mr. Zhang Xinsheng, mataimakin ministan ba da ilmi na kasar Sin, da Mr. Hu Zhanfan, mataimakin shugaban babbar hukumar watsa labarai da sinima da talebijin ta kasar Sin, da madam Xu Lin, direktar ofishin karamar kungiyar shugabanci na kasar Sin wajen yada harshen Sinanci tsakanin kasa da kasa, da jami'an diplomasiya na kasashen 14 da ke kasar Sin, da wakilan musamman da aka gayyace su daga dakunan ba da darassun Confucius sun halarci bikin da aka yi a wannan rana.

Madam Xu Lin ta taya murnar kafa kolejin watsa labarai ta Confucius, ta bayyana cewa,

"Ba shakka Kolejin ba da darassun Confucius ta hanyar watsa labarai zai ba da babban amfani fiye da yadda muka yi a wannan fanni wato koleji ba ta watsa labarai ba." (Umaru)


1 2