Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-06 18:39:22    
An kafa kolejin watsa labarai ta Confucius ta farko a kasar Sin

cri

Yau ran 6 ga wata a nan rediyonmu wato Rediyon kasar Sin, an kafa kolejin watsa labarai ta Confucius ta farko ta kasar Sin a hukunce, madam Chen Zhili?wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin da hannunta na kanta ne ta cire labule da ke alamanta bude kolejin. Nan gaba, masu sauraronmu da ke kasashen waje za su iya koyon Sinanci da sauki wato ta hanyar sauraran shirye-shiryen da kolejin watsa labarai ta Confucius ya bayar ko kuma karanta shafuffukan Internet na wannan koleji. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta cikakken bayani game da wannan labari.

Rediyon kasar Sin da babbar hukumar kolejin Confucius su ne suka kafa kolejin watsa labarai na Confucius ta hanyar hadin gwiwa. Yau wato ran 6 ga wata, madam Chen Zhili?wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin da hannunta na kanta ne ta cire labule da ke alamanta bude kolejin.

An labarta cewa, kolejin watsa labarai na Confucius za ta koyar da Sinanci bisa littafin koyarwa bai daya na wannan harshe ta hanyar ba da darasi cikin aji, da rediyo da kuma ta hanyar internet, kuma za ta ba da darussa ga dalibai masu koyon harshen Sinanci da ke wurare daban-daban na duniya ta hanyar yin amfani da harsuna iri 38 bisa manufarta ta yada al'adun kasar Sin.

A gun bikin cire labule, Mr. Wang Gengnian, shugaban rediyon CRI ya bayyana cewa, rediyon kasar Sin yana da fasahohi da yawa wajen koyar da harshen Sinanci ga masu karatu na kasashen waje, yanzu sassan watsa labarai na harsuna iri 38 na rediyon dukkansu sun bude filin koyar da Sinanci cikin shirye-shiryensu, sun yi haka ne domin biyan bukatun masu sauraronmu miliyoyi wajen koyon harshen Sinanci. Ya ce,"Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, Rediyon kasar Sin ya bi hanyar zamani domin gudanar da aikin watsa labarai, ya ba da shawara ga masu sauraro na kasashen waje cewa, ya fi kyau su koyi Sinanci ta hanyar yin amfani da yarensu na kansu, ko kuma ta hanyar rediyo, da tsarin internet, da kulob din masu sauraro da ke ko ina na manyan nahiyoyi 5, kuma rediyon CRI yana kokarin kafa tsarin yada harshen Sinanci da al'adun kasar Sin ta hanyoyi daban-daban. Kafuwar Kolejin watsa labarai ta Confucius ba shakka za ta sa kaimi sosai ga aikin yada harshen Sinanci tsakanin kasa da kasa da kara yin mu'amala tsakanin Sin da kasashen wajen wajen al'adu."

1 2