Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 17:04:10    
Sakin jikinka a Shangri-la

cri

Mashayar Ana da otel din 'Laokezhan' da muka yi bakunta dukansu na cikin garin Dukezong, wanda gari ne mafi tsufa a Shangri-la, yana da tsawon shekaru dubu 1 ko fiye. A kan kira shi gari mai dimbin fararen duwatsu, saboda dukan dakunan da ke cikinsa an shafe su da farar kasa a waje.

In ka kawo wa Shangri-la ziyara, kada ka manta da dandana abinci mai dadin ci na wurin. Dakin cin abinci na Arro Khampa wuri ne mafi dacewa a gare ka. An yi wa dakin cin abincin ado kamar yadda gida yake. Mai dakin ya ajiye tsoffin kayayyakin daki a cikin wannan dakin cin abinci, haka kuma, a kan tebur kuwa, kwafuna da kananan tabarmin da ke karkashinsu na da kayatarwa sosai. Sabis din na dakin cin abincin suna karbar baki da hannu biyu biyu. Wata budurwa mai suna Zhuoma, 'yar kabilar Zang, ta rera mana wata wakar gargajiya ta kabilarta. Bhaskar Uday, wani kuku ne da ke aiki a dakin cin abinci na Arro Khampa, ya zo daga kasar Nepal. Ko abinci iri na kabilar Zang ko na Nepal ko na kasar Indiya ko na kasar Sin, ya iya dafa su gaba da baya, wannan kuku ya yi hira da mu cikin Sinanci.

'Na yi shekara guda da rabi ina aiki a wajen. A da na taba aiki a lardunan Gansu da Qinghai da Sichuan. Abokaina da yawa sun ba ni labarin wannan wuri, shi ya sa na zo nan. Shangri-la wuri ne da na fi kauna. A galibi dai ya yi kama da garina na Nepal.'

Bayan da muka fita daga dakin cin abinci na Arro Khampa, ko da yake dare ya yi duhu, amma ba a yi tsit a garin Dukezong ba. A babban filin titin Sifangjie da ke cibiyar tsohon birnin, mutane suna raye-raye, suna wake-wake. Irin wannan hali ya sa mu shiga cikin cunkuson mutane, muna rawa tare da su.


1 2