Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 17:04:10    
Sakin jikinka a Shangri-la

cri

A Shangri-la na lardin Yunnan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, hasken rana ya fado a kan hanyoyin dutse masu gargada da yamma. A lokacin da muke yawo a kan hanyar, mun saurari wannan kidan da kuke saurara. Bisa wurin da kidan ke fitowa, mun shiga wata mashaya. Sunan mai mashayar shi ne Adu, shekarunsa ya wuce 30 da haihuwa. Wannan kida mai suna kyakkyawan Shangri-la kida ne da ya fi so. Adu ya kan busa wannan kida da kayan kida na Saxophone a gaban bakin da suke fitowa daga nesa. A lokacin da muke hira, ya ce, a can da bai yi tsammani cewa, ya tsai da kudurin zama a Shangri-la ba, sai bayan ziyararsa a wannan wuri ba. Ya ce, 'Na kawo wa Shangri-la ziyara a shekarar 2003. Na yi wata guda ko fiye ina yawon shakatawa a wajen. A lokacin, na shiga soyayya da wannan wuri. Shi ya sa na nemi wani daki domin yin hutu a wajen a ko wace shekara. Sannu a hankali, na raya gidana zuwa dakin shan giya.'

Wato ke nan, Adu ya tsugunad da kansa a Shangri-la, ya kuma yi aure, yana da 'yarsa. Ya nada wa mashayarsa sunan Ana, ma'anar Ana a bakin 'yan kabilar Zang ita ce giya.

Dashan, wata abokiya ce da muka yi abota da ita a Shangri-la. Asalin sunanta shi ne Yangjin, ita 'yar kabilar Zang ce da ta yi zama a Shangri-la tun lokacin yarantakarta. Bayan da ta yi wani tsawon lokaci tana karatu da aiki a biranen Beijing da Shanghai, ta koma garinta, ta bude wani karamin otel mai suna Laokezhan, wato tsohon otel ko kuma Shangri-la Old Town Cobbler's Hill Old Inn a Turance. Ginin otel din na da tsawon shekaru a kalla 300. Mutane kan ji sakin jiki a lokcin da suke zama a cikin dakuna fiye da goma, wadanda Dashan ta yi kwaskwarima da kuma kayatar da su a tsanake.

Otel din 'Laokezhan' ba kawai wani otel ne kawai da Dashan ke tafiyar da shi ba, har ma shi ne wata Aljanna da ta yi abokanta da saura, a ciki kuma, akwai dimbin bakin ketare. Malam Thomas Blake da abokansa sun zo ne daga kasar Australia, sun yi kwanaki da dama suna yawo a tsohon birnin da ke Shangri-la. Sun fi nuna sha'awa kan wannan otel din 'Laokezhan' mai nuna sigar musamman da kuma mazaunan tsohon birnin. Sun ce, 'Mun yi kwanaki 2 muna yada zango a wajen. Mun taba ziyarar wurare da yawa. Haka kuma, mun dandana abincin wurin da yawa. Wurin nan kayataccen wuri ne mai ban mamaki. Otel din 'Laokezhan' na da matukar kyan gani. Mun taba shiga otel-otel da yawa, amma mun fi son otel din 'Laokezhan'. Shi wani tsohon gini ne, amma dakunansa na da sabon ado da kuma tsari'

1 2