Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 11:01:16    
Ya kamata nahiyar Afirka ta fuskanci cutar AIDS tare da jaruntaka

cri

Dangane da irin yanayin da ake ciki, wasu kasashen Afirka suna kaddamar da hanyoyi iri iri domin gwajin cutar AIDS, kaman yin gwaji kai tsaye cikin gida, wadanda ke dacewa da muradin mutane. Tun daga watan Yuni na shekarar 2006, kimanin mutane dubu 10 a kasar Zambiya sun karbi gwajin cutar AIDS ta wadannan hanyoyi.

Bugu da kari, a kasashen Uganda, da Kenya da Zimbabwe wadanda suke da matukar karfi wajen fadakar da jama'a da baza amfanin robar hana daukar ciki, an sassauta saurin yaduwar cutar kanjamau. Misali a kasar Uganda, yawan mutane wadanda suke kamu da cutar ya ragu daga kashi 30 daga cikin dari har zuwa kashi 6.5 daga cikin dari a halin yanzu.

Wani likitan aikin soja wanda ya dade yana aikin warkar da cutar AIDS ya fadi cewa, "Cutar kanjamau daya daga cikin dubun dubatar cututtuka a duk duniya, a zahiri dai, ba ta da banbanci da sauran cututtuka. Shi ya sa kamata ya yi mu fuskanci wannan cuta yadda ya kamata, domin cimma nasarar yaki da cutar AIDS." Yana fatan jama'a za su fuskanci cutar kanjamau tare da jaruntaka.

Domin yin marhabin da ranar yaki da cutar sida ta kasa da kasa wato ranar 1 ga wata, daga ranar 22 ga watan Nuwamba, an ajiye kwalaben gilashin dake makare da wasikun tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu Nelson Rolihlahla Mandela da yawansu ya kai miliyan guda a wurare daban daban na kasar, domin yin kira ga jama'a da su dauki hakikanan matakai wajen yaki da cutar kanjamau. A cikin wasikarsa, Mr. Mandela ya rubuta cewar, cutar kanjamau ba ma kawai wata cuta ba, har ma ta zama batun ikon jama'a. Shi ma ya yi kira ga mutane da su bada gudummawarsu ta hanyar bada kyautar kudi, ta yadda za a yaki da cutar AIDS kafada da kafada.

Kazalika, kwanan baya, wasu fitattun mutane na kasashen Afirka sun yi dafifi a kasar Zambiya, inda suka bada sanarwa ga dukkan nahiyar Afirka cewar, "Mun taba ficewa daga zaman bayi, mun taba juya mulkin mallaka na Turawa, mun taba samun galaba kan yunkurin wariyar al'umma. Amma a halin yanzu, kamata ya yi mu yi amfani da jaruntaka da cikakken karfi irin na lokacin da, mu hada kanmu domin fuskantar kalubalen da cutar AIDS ke jawo mana. "(Murtala)


1 2