Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-04 11:01:16    
Ya kamata nahiyar Afirka ta fuskanci cutar AIDS tare da jaruntaka

cri

Assalam alaikum! Jama'a masu sauraro, barkanku da war haka! Barkanmu da kuma sake saduwa da ku a cikin shirinmu na yau na "Afirka a Yau". A albarkacin ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don yaki da cutar AIDS a karo na 20, wato Sida, za mu gabatar muku da wani bayanin musamman mai lakabi haka, ya zama tilas nahiyar Afirka ta fuskanci cutar AIDS tare da jaruntaka.

A cikin gwagwarmayar da ake yi ta yunkurin yaki da cutar sida ko kanjamau a duk fadin duniya, mutanen yankuna da dama na nahiyar Afirka suna zama ne ba tare da cikakken ilimi kan cutar ba, suna fargabar wannan cuta, haka kuma, sun ki a yi musu gwajin jini.

Bisa wani kwarya-kwaryar rahoton da Majalisar Dinkin Duniya ta bayar, an ce, a halin yanzu, a shiyyar dake kudu da hamadar Sahara, adadin mutane wadanda suka kamu da kwayar cutar kanjamau ya kai kimanin miliyan 22.5, wanda ya kai sulusani na daukacin mutane wadanda suka kamu da cutar a duk fadin duniya. Yanzu, cutar kanjamau ta rigaya ta maye gurbin yake-yake da fadace-fadace, ta fara zamanto "mummunar mai kisa ta farko" a nahiyar Afirka. Alal misali, a kasar Zambiya, bisa alkaluman da kwamitin yaki da cutar AIDS na kasar ya bayar, an ce, a duk doron kasar, mutanen da suka kamu da cutar ya kai kimanin kashi 16 daga cikin dari, wato a cikin mutane shida, akwai daya daga cikinsu wanda ya kamu da kwayar cutar kanjamau. Amma cikin jimlar adadin mutanen kasar, akwai kashi 13 bisa dari kawai wadanda suka yi gwajin cutar AIDS bisa son ransu, a sa'i daya mutane da dama ba sa son yin wannan gwaji ko da yake ba a bukatar biyan kudi. A ganinsu, idan suna sane da cewar sun kamu da cutar kanjamau, to, ba su da jaruntakar cigaba da zamansu.

A wani asibitin dake babban birnin kasar Zambiya wato Lusaka, wata gyatuma wadda ba ta jin dadin jikinta sosai, ta ki a yi mata gwajin jini faufau. Ta gayawa likita cewar, ta dade da zaman gwauruwa. Muddin dai tana sane da cewar ta kamu da AIDS, to, za ta rasa abun da za ta yi, ba ta san yadda za ta fuskanci dangoginta da aminanta ba, kuma ba ta san yadda za ta yi domin fuskantar banbanci da sauran mutane za su nuna mata ba.

Wani likita na asibitin aikin horaswa na jami'ar Zambiya ya gabatar da cewa, a shekarun 90 na karnin da ya shige, wannan asibiti ya gwada jinin mutane cikin sirri ba tare da sanar da su ba. A karshe dai, bayan da mutane da dama suka gane cewar sun kamu da cutar kanjamau, sun ki karbar aikin jinya daya bayan daya saboda bakin cikinsu, har ila yau kuma wasunsu sun kashe kansu.

1 2