Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-12-03 19:07:02    
Kasar Sin na ba da tabbaci ga ingancin abincin da take samu daga ruwa

cri

An dauki matakai a wurare daban daban na kasar Sin don kara kula da ingancin abincin da ake samu daga ruwa. Lardin Jiangxi yana daya daga cikin manyan lardunan kasar Sin da ke fitar wa kasashen waje abinci mai yawa da suke samu daga ruwa. Yana fitar da irin abincin nan musamman zuwa kasashen Amurka da Japan da kasashen kungiyar tarayyar Turai da sauran kasashe da shiyyoyi. Malam Xu Youguang, wani jami'in hukumr kula da harkokin abincin da ake samu daga ruwa ta lardin ya bayyana cewa, lardinsa ya kara kokari wajen kula da ingancin abincin da ake samu daga ruwa don ba da tabbaci ga abincin da ake fitarwa zuwa kasashen waje. Ya kara da cewa, "yanzu, muna gudanar da tsarin rajistar abincin da ake samu daga ruwa, mu hana a yi amfani da haramtattun magungunan kashe kwayoyin cuta wajen samar da abincin da ake samu daga ruwa a duk wuraren lardin. Haka kuma mu bukaci wuraren samar da abincin da su yi rubuce-rubuce a kan yadda suke samar da abincin, ta haka za mu iya gano yadda ake samar da su. Daga karshe kuma muna kara kokari wajen yin bincike-binciken ingancin abincin da ake samu daga ruwa yadda muke ga dama"

Malam Cui Lifeng, mataimakin babban direktan hukumar kula da aikin kamun kifi na ma'aikatar aikin noma ta kasar Sin ya ce, nan gaba, kasar Sin za ta dauki mataikai wajen hana yin amfani da haramtattun magungunan kashe kwayoyin cuta wajen samar da abinci da ake samu daga ruwa. Ya ci gaba da cewa, "za mu bayar da umurni ga duk wuraren da ke da aibobi wajen samar da abincin ruwa su kawar da su a tsanake, mu yanke hukunci mai tsanani a kan kamfanonin da suka saba wa dokoki da ka'idoji. A sa'I daya za mu jera sunayen kamfanonin da za mu sanya musu ido kwarai, kuma za mu kara kokari wajen yin bincike-bincike kan kamfanonin wadanda suka saba wa dokoki da ka'idoji yadda muka ga dama. "

Ya fayyace cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da yada hanyoyin da ake bi wajen samar da abinci mai inganci daga ruwa, ta yadda za ta samar da abinci mafi inganci da ake samu daga ruwa domin masaya na gida da waje. (Halilu)


1 2