Kasar Sin tana daya daga cikin manyan kasashe masu albarkatun abincin da ake samu daga ruwa a duniya. Yawan irin wadannan abincin da kasar ta samu ya kai tan miliyan 53 a shekarar bara, wato ke nan ya kai matsayi na farko a duniya. Yayin da take kokari sosai wajen bunkasa harkokin samun abinci daga ruwa, gwamnatin kasar Sin ta tsai da ka'idoji kan ingancin abincin da ake samu daga ruwa a fannonin muhallin wuraren samun abinci da na sayar da su da amincewa da su, ta haka kasar Sin ta gaggauta kai ma'aunin kasa da kasa.
Malam Cui Lifeng, mataimakin babban direktan hukumar kula da aikin kamun kifi na ma'aikatar aikin noma ta kasar ya bayyana cewa, a galibi dai, ana ba da tabbaci ga ingancin abincin da ake samu daga ruwa. Ya ce,
"a cikin shekarun nan da suka gabata, kasar Sin ta yi ta daga matsayin ingancin abincin da take samu daga ruwa sannu a hankali. Kashi 97 cikin dari na abincin da kasar ke samu daga ruwa sun dace da ma'aunin ingancinsu a cikin shekaru hudu da suka wuce a jere. Saboda haka ana iya cewa, a galibi dai abincin da kasar Sin ke samu daga ruwa yana da inganci, ana iya cinshi cikin kwanciyar hankali."
An ruwaito cewa, kasar Sin ta riga ta inganta dokoki kan al'amuran da abin ya shafa, a fili ta hana a yi amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta kamar Malachite Green a Turance wajen kiwon kifaye da makamantansu. Kana kuma ta yada hanyoyin da ake bi wajen kiwon kifaye da makamantansu yadda ya kamata, kuma bisa ma'aunin da aka kafa a kasashen masu shigar da su daga kasar Sin.
1 2
|