Amma duk da haka, Sin na cigaba da fuskantar hali mai tsanani a wajen tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba. Mr.Xie Zhenhua ya ce, wasu wurare ba su gudanar da aikinsu kamar yadda ya kamata ba, kuma ba su tabbatar da shirinsu na tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba ba. Idan ba a canza irin wannan hali yadda ya kamata ba, to, abin zai haddasa manyan illoli ga tabbatar da shirin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba a nan gaba.
Sabo da haka, kwamitin kula da raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin da sassan da abin ya shafa sun tsara shirin aiwatar da tsarin binciken yawan makamashin da aka yi amfani da shi a wajen GDP da tsarin ma'aunan kirga makamashin da aka yi amfani da su wajen GDP da shirin aiwatar da tsarin sa ido da dai sauransu, kuma yanzu majalisar gudanarwa ta Sin ta riga ta amince da shirye-shiryen.
Mr.Xie Zhenhua ya yi nuni da cewa, shirye-shiryen sun kafa wani cikakken tsari na yin kididdiga da sa ido da bincike a kan yadda ake tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli. Ya ce,"tsarin bincike ya gabatar da cewa, za a mika sakamakon karshe na bincike ga muhimman hukumomin kula da mahukunta da kwamitocin kula da kadarorin kasa na matakai daban daban, kuma za a mayar da shi a matsayin wani muhimmin abu na bincike yadda hukumomi daban daban da shugabanninsu da kuma kamfanoni mallakar gwamnati suke gudanar da aikinsu. Wadanda ba su sauke nauyinsu ba kuma, za mu soke izninsu na zama fitattu a wannan shekara. Sa'an nan, za a daina amincewa da ayyukan da za su iya yin amfani da makamashi mai yawa ko kuma gurbata muhalli da za su gudanar. " (Lubabatu) 1 2
|