Yau a nan birnin Beijing, Mr.Xie Zhenhua, mataimakin shugaban kwamitin kula da raya kasa da gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar da muke ciki, Sin ta dauki jerin tsauraran matakai a fannin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli, kuma ta kara samun nasara. Ya ce, kwanan nan, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da shirin da sassan da abin ya shafa suka tsara dangane da yin kididdiga da sa ido da kuma bincike a kan yadda ake tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba, wanda kuma ya bayyana cewa, Sin ta shiga wani mataki na tabbatar da shirin tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli.
A cikin wannan shekara, gwamnatin kasar Sin ta kara karfin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli, kuma wurare da hukumomi daban daban su ma sun mayar da aikin tsimin makamashi da rage fitar da abubuwa masu gurbata muhalli a wani muhimmin matsayi, Mr.Xie Zhenhua ya ce, yanzu ana ta kara tabbatar da manufofi da matakai daban daban na tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu gurbata muhalli, har ma an samu nasara sosai. Ya ce, "A shekarar da muke ciki, mun dauki matakai takwas a wajen tsimin makamashi da rage fitar da sinadarai masu guba, kuma yanzu ana tabbatar da matakan a kai a kai. Daga watan Janairu har zuwa watan Satumba, yawan makamashin da aka yi amfani da shi don samun kudi daga samar da kayayyaki wato GDP, ya rage da kashi 3%, a yayin da sulfur dioxide da COD da aka fitar sun ragu duka."
1 2
|