Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 18:22:30    
Ana gudanar da aikin kiyaye muhalli a madatsar ruwa ta Sanxia yadda ya kamata

cri

Mr.Wang Xiaofeng ya kuma ba da wasu adadai don bayyana kyakkyawar rawa da madatsar ruwa ta Sanxia ke takawa. Na farko, sakamakon gina madatsar ruwa ta Sanxia, ana iya fuskantar ambaliyar ruwa mai tsanani da ba safai a kan gamu da ita har cikin shekaru 100 ba. Na biyu, bayan da aka fara aiki da madatsar ruwa ta Sanxia, gaba daya yawan wutar lantarki da ta samar ya riga ya wuce kw biliyan 200. Bayan da aka kammala aikin harhada injunan bunkasa wutar lantarki kuma, madatsar ruwan zai iya zama wani babban ginshiki a wajen samar da wutar lantarki ga gabashin kasar Sin da tsakiyarta da kuma kudancin kasar. Na uku, bayan da madatsar ruwan ta fara datse ruwa, kayayyakin da jiragen ruwa ke jigilarsu da suka wuce madatsar ruwan a duk shekara sun wuce ton miliyan 50, a maimakon ton miliyan 18 kawai kafin a datse ruwan, wanda zai sa kaimi sosai ga bunkasuwar zirga-zirgar jiragen ruwa a kogin Yangtse.

A matsayin daya daga cikin ayyukan datse ruwa da bunkasa wutar lantarki mafi girma a duniya, tasirin da madatsar ruwa ta Sanxia za ta iya kawo wa muhalli na jawo hankulan jama'a har kullum. A gun taron manema labarai, Mr.Wang Xiaofeng ya ce, gwamnatin kasar Sin tana dora muhimmanci sosai a kan kiyaye muhalli a madatsar ruwa ta Sanxia, kuma bisa kokarin da hukumomi daban daban suka yi, an cimma manyan nasarori a wajen kiyaye muhallin wurin. Ya ce,"bisa binciken da aka yi bayan da madatsar ruwa ta Sanxia ta fara datse ruwa, an ce, tasirin da madatsar ruwan ke kawo wa muhallin wurin na cikin yadda ake hasashe a cikin rahoton bincike na wannan shekara. Yanzu muhallin wurin da ake gudanar da gine-gine da kuma wurin da aka zaunad da mutanen da aka kwashe duka suna da kyau, kuma an shawo kan zaizayewar kasa yadda ya kamata, yanzu ruwan kogin Yangtse da ke cikin madatsar ruwan na da inganci. Bayan haka, rairayin da suka shiga madatsar ruwan sun ragu, kuma ba a gano alamun da za su iya haddasa girgizar kasa ba. Ban da wadannan, ana kuma ba da kariya ga dabbobi da tsire-tsire masu daraja da ke madatsar ruwan yadda ya kamata."


1 2