Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 18:22:30    
Ana gudanar da aikin kiyaye muhalli a madatsar ruwa ta Sanxia yadda ya kamata

cri

A yanzu haka dai, an cimma babbar nasarar gina babbar madatsar ruwa ta Sanxia, wadda ta kasance daya daga cikin ayyukan datse ruwa da samar da wutar lantarki mafi girma a duniya. Ya zuwa watan Satumba na shekarar da muke ciki, ana gudanar da ayyukan datse ruwa da harhada injunan samar da wutar lantarki da kuma kwashe mutane yadda ya kamata, kuma daga cikinsu, an kusan kammala aikin harhada injunan samar da wutar lantarki. A sa'i daya kuma, ana gudanar da aikin kiyaye muhalli a madatsar ruwan yadda ya kamata.

A gun taron manema labarai da ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya kira a ranar 27 ga wata, Mr.Wang Xiaofeng, shugaban ofishin kula da aikin gina madatsar ruwa ta Sanxia na majalisar gudanarwa ta Sin, ya bayyana cewa, yanzu ana gudanar ayyukan gina madatsar ruwa ta Sanxia kamar yadda aka tsara kuma yadda ya kamata, har ma an cimma manyan nasarori. Ya ce,"ana gudanar da aikin datse ruwa da aikin harhada injunan samar da wutar lantarki da kuma aikin kwashe mutane yadda ya kamata, kuma an tabbatar da ma'aunin ruwa da ya kai mita 156 a madatsar ruwan, an kuma kwashe mutanen da yawansu da ya kai miliyan, yanzu madatsar ruwa ta Sanxia na kara taka gaggarumar rawa a wajen magance ambaliyar ruwa da bunkasa wutar lantarki da zirga-zirgar jiragen ruwa da kuma kiyaye muhalli. Bayan haka, jama'ar da aka kwashe su daga wurin ma suna ta samun kyautatuwar zaman rayuwa sannu a hankali, kuma ana ta samun cigaban tattalin arziki da zaman al'umma a shiyyar da madatsar ruwan ke ciki.


1 2