Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-27 16:37:07    
Cibiyar wasannin ruwa ta kasar Sin

cri

Bugu da kari kuma, a cikin wannan cibiyar wasannin ruwa, an shafa irin wadannan abubuwan musamman a jikin bango. Mutane na iya ganin irin wadannan abubuwan musamman da aka yi zane-zanen halittun ruwa a kansu a cikin tsabataccen ruwa a wurin ninkaya, saboda haka 'yan kallo sun yi kama da shiga duniyar halittun ruwa. Kallon gasannin ninkaya a nan na da ban mamaki da sha'awa. A cikin wannan cibiya, an samar da kujeru dubu 17 na 'yan kallo, a ciki kuma, wasu dubu 6 na din din din, za a samar da karin kujeru dubu 11 na wucin gadi, wadanda za a cire su bayan taron wasannin Olympic na Beijing.

Don me abubuwan musamman da aka shafa a waje da wannan cibiyar wasannin ruwa suka kawo wa mutane mamaki? Dalilan su ne saboda da farko irin wadannan abubuwan musamman da ake iya kallo ta ko wace fuska na da kwari sosai, har ma ko da wasu mutane sun sha tsalle a kansu, ba za su iya karye su ba. Ban da wannan kuma, wadannan abubuwan musamman na iya tsabta kanta domin suna da sumul kwarai, har ma rairayi da abubuwan kazanta ba su iya tsayawa a kansu ba. Dadin dadawa kuma, wadannan abubuwan musamman na iya tattara ruwa a lokacin da ake ruwa, haka kuma, in ana rana, sun iya shigo da hasken rana da yawa, ta haka za a yi tsimin makamashi.


1 2 3