Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-11-21 17:17:58    
An kammala gina katafaren dandalin wasan kwaikwayo na kasar Sin da kuma soma nuna wasanni

cri

Wani Bafaranshe mai suna Paul Andreu shi ne ya zayyana wannan katafaren dandali mai zubi da tsarin kwai, dandalin wanda ke yamma da Tian'anmen Square kuma ke cibiyar birnin Beijing , yana dab da babban dakin taruwar jama'a na birnin Beijing, tun daga shekarar 2001 da aka soma gina shi, sai mutanen rukunoni daban daban suka mai da hankulansu a kai .

Babban ginin dandalin nan da aka gina bisa fasali mai zubi tsarin kwai, tsayinsa ya kai mita 47, a kewayensa, da akwai tabkin da aka haka tare da lambun shan iska. da dare, ana iya ganin inuwar babban ginin a cikin ruwan tabkin , ga sifarsa ta kwai ta yi tamkar yadda kwan lu'u-lu'u mai kyalkyali tare da hasken fitilun tamkar yadda taurarin da ke sararin samaniya, kai, katataren dandalin nan na da kyaun gani yake sosai da sosai.

Wani shugaban kula da aikin ginawar dandalin Mr Peng Chengjun ya bayyana cewa, a lokacin da muke gina babban ginin, mun gamu da wahaloli da yawa wajen fasahohin ginawa, alal misali, game da rumfar ginin nan, mun gina ta ne da bakin karfe , sa'anan kuma jinginar ginin su ma da bakin karfe, yanzu a nan birnin Beijing, ba wanda ya kai girmansa, yawan fadinsa ya kai murraba'in mita dubu 25.5, yadda za a hada shi? wani injiniya ya bayyana cewa, ya yi aikin ginawa, amma bai taba yin irin aiki mai wuya kamar wannan ba.

Babban ginin nan yana dauke da manyan dakuna uku, wato dakin kallon wasannin kwaikwayo da ake nunawa ta hanyar rera wakoki da dakin saurarar wake-wake da kide-kide da kuma wani karin dakin nuna wasannin kwaikwayo, kuma yawan kujerunsu ya kai 5400 ko fiye.

Bayan gwajin nune-nunen wasannin fasahohi, za a shirya nune-nunen wasanni na kasar Rasha da ta Amurka da ta Faransa da ta Italiya da sauransu 6 ko fiye.(Halima)


1 2